Gwamnatin Tinubu Ta Sanya Jiragen Shugaban Kasa 3 a Kasuwa, Ta Fadi Dalili

Gwamnatin Tinubu Ta Sanya Jiragen Shugaban Kasa 3 a Kasuwa, Ta Fadi Dalili

  • An sanya wasu tsofaffin jiragen shugaban ƙasa guda uku na gwamnatin tarayyar Najeriya a kasuwa
  • An tattaro cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin sayar da jiragen saboda kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da su
  • Sayar da jiragen zai sanya jiragen shugaban ƙasan su ragu inda a yanzu yake da jirage guda shida da jirage masu saukar angulu guda huɗu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sanya a sayar da jiragen shugaban ƙasa guda uku da suka tsufa.

An tattaro cewa sayar da jiragen zai rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Gwamnatin Tinubu za ta siyar da jiragen shugaban kasa
Jirage guda uku gwamnatin tarayya ta sanya a kasuwa Hoto: @imranmuhdz
Asali: Twitter

Sayar da jiragen zai rage yawan jiragen da ke cikin jerin jiragen saman fadar shugaban ƙasa da kusan rabi, domin a halin yanzu akwai jiragen sama guda shida da jirage masu saukar ungulu guda huɗu, cewar rahoton TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiragen sun haɗa da Boeing 737 Boeing Business Jet (BBJ), Gulfstream G550, Gulfstream GV, Falcon 7x guda biyu da Challenger CL605 guda ɗaya.

An tattaro cewa kusan rabi daga cikin jiragen ba su yin aiki ko sun lalace.

Waɗanne jirage za a sayar?

Jiragen shugaban ƙasa na Boeing 737 Boeing Business Jet (BBJ), Gulfstream guda ɗaya da Falcon 7x guda ɗaya aka sanya a kasuwa.

Rahotanni sun ce an sanya wani kamfani a Amurka mai suna JetHQ a matsayin dillalin siyar da jiragen guda uku.

A cewar masu ido kan batun sayar da jiragen, kuɗaɗen da aka samu daga siyarwar za a yi amfani da su wajen siyan sabon jirgi.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

Meyasa Tinubu ya ce a siyar da jiragen?

Jaridar The Nation ta ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sayar da jiragen ne saboda kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da su.

An tattaro cewa gwamnatin Najeriya ta kashe sama da dala miliyan 5 a matsayin kuɗaɗen kula da jiragen a ƴan watannin da suka gabata.

Hadimin Tinubu ya caccaki Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta caccaki Peter Obi kan kalaman da ya yi dangane da shirin siyan sabon jirgin sama ga Shugaba Bola Tinubu.

Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya caccaki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar Labour Party (LP) kan batun siyo jirgin saman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel