"Yana da Ɗure Kai," Falana Ya Faɗi Kuskuren da Aka Yi a Hukuncin Shari'ar Sarautar Kano

"Yana da Ɗure Kai," Falana Ya Faɗi Kuskuren da Aka Yi a Hukuncin Shari'ar Sarautar Kano

  • Femi Falana SAN ya soki hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a shari'ar sarautar Kano, ya ce akwai ruɗani a lamarin
  • Fitaccen lauyan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam ya ce hukuncin yana da ɗaure kai domin kotun koli ta hana kotunan tarayya tsoma baki a sha'anin sarauta
  • Wannan na zuwa ne bayan alkalin babbar kotun tarayya ya soke matakin mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Fitaccen lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana SAN ya ce hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano yana da ɗan ɗaure kai.

A wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, Femi Falana ya ce kotun koli ta yanke hukuncin cewa manyan kotunan tarayya ba su da hurumin sauraron shari’ar sarauta.

Kara karanta wannan

"Akwai rikitarwa": Farfesan Lauyoyi, Yadudu ya gano kuskure a hukuncin shari'ar sarautar Kano

Femi Falana.
Hukuncin Kotu a kan rikicin masarautar Kano yana da rudani in ji Falana Hoto: @instablog9ja
Asali: Twitter

Wane hukuncin babbar kotun ta yanke?

Idan ba ku manta ba a jiya Alhamis, babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke matakan da Gwamna Abba Kabir ya ɗauka yayin mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Muhammad Liman ya ce waɗanda ake kara sun take umarnin wucin gadin da kotun ta bayar a lokacin aiwatar da sabuwar dokar masarauta 2024.

Sai dai alkalin kotun ya ce umarnin nasa bai shafi ingancin dokar masarautar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Falana ya gano kuskure a hukuncin shari'ar

Da yake martani kan haka, Falana ya ce kotun kolin ta fitar da wasu hukunce-hukunce daban-daban guda biyu wadanda suka takaita ikon kotun tarayya kan shari'ar sarauta.

Babban Lauyan ya bayyana cewa hukuncin na kotun ƙoli ya shafi dukkan masarautun kasar nan.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarauta a Kano, wani gwamna ya rage wa sarakuna ƙarfin iko

"Hukuncin Kano yana da ɗan ɗaure kai. Amma abu mafi muhimmanci da alkalin ya manta shi ne hukuncin kotun koli na hana manyan kotunan tarayya tsoma baki a shari'ar sarauta."
"Ba zai yiwu a fake da sunan take haƙƙin ɗan adam ba, a saurari alkalin, na fahimci ya fi jaddada wajibcin mutunta umarnin doka. Duk ƙasar da ke aiki da doka, ta san hukuncin kotun ƙoli ya shafi kowa."

- Femi Falana SAN

Gwamna Sule ya ragewa sarakuna iko

A wani rahoton kuma Gwamna Abdullahi Sule ya hana sarakuna bayar da shaidar izinin haƙar ma'adanai ga mutanen ba su cika sharuɗɗa ba a jihar Nasarawa.

Abdullahi Sule ya gargaɗi sarakunan kan barazanar da hakan kan iya haifarwa a jihar idan har ba a gaggauta ɗaukar mataki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262