Ana Tsaka da Rigimar Sarauta a Kano, Wani Gwamna Ya Ragewa Sarakuna Ƙarfin Iko
- Gwamna Abdullahii Sule ya hana sarakuna bayar da shaidar haƙar ma'adanai ga mutanen ba su cika sharuɗɗa ba a jihar Nasarawa
- Abdullahi Sule ya gargaɗi sarakunan kan barazanar da hakan kan iya haifarwa a jihar idan har ba a gaggauta ɗaukar mataki ba
- Ya ce masu haƙar ma'adanai ba kan ƙa'ida ba ke jawo rashin zaman lafiya domin ɗauke hankalin mahukunta daga albarkatun ƙasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Yayin da hankula suka fi karkata kan rigimar sarautar Kano, Gwamna Abdullahi Sule ya ɗauki mataki kan sarakuna a jihar Nasarawa.
Gwamna Sule ya gargaɗi sarakuna su guji bayar da takardar izinin haƙo ma'adanai ga mutanen da ba su cika sharuɗɗa ba a kananan hukumomi 13 na jihar.
Abdullahi Sule ya bayyana babbar barzanar tsaro da jihar ke fuskanta sakamakon bada izinin ga waɗanda basu dace ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a lokacin da ya karbi bakuncin majalisar sarakunan jihar karkashin jagorancin mataimakin shugabanta, Sarkin Keffi, Dokta Shehu Chindo Yamusa III.
Gwamna Sule ya faɗi illar bada izinin
Yayin da yake jawabi ga sarakunan a gidan gwamnatinsa da ke Lafiya, Sule ya nuna damuwa kan kwararar haramtattun masu haƙar ma'adanai a jihar.
Ya ce hakan ka iya zama babbar barazana ga tsaro matukar ba a yi gaggawar tsohe duk wata hanyar shigowar masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.
Ya bukaci sarakunan da su yi taka-tsan-tsan da daidaikun mutane da ke amfani da yanayin tattalin arziki wajen tayar da zaune tsaye a wuraren hakar ma’adanai.
Abin da Gwamnan Nasarawa ya fadawa Sarakuna
"Ba abin da ke kawo rashin zaman lafiya kamar haƙar ma'adanai, ita ce hanya mafi sauƙi da mutane ke samun kuɗi.
"Musamman waɗanda babu kishin jiharmu a zuciyarsu burinsu kawai su hana zaman lafiya ta yadda za su ci gaba da haƙo ma'adanai ba tare da an waiga kansu ba."
- Abdullahi Sule.
Bugu da ƙari, gwamnan ya shaidawa sarakunan cewa ana ci gaba da gano albarkatun ƙasa a jihar kuma kamfanoni na nuna sha'awar zuba hannun jari, Channels tv ta ruwaito.
Gwamnatin Kano za ta ɗaukaka ƙara
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano karƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke naɗin Muhammadu Sanusi II.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Alhaji Baba Ɗantiye ne ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya turawa manema labarai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng