Ana Fama da Tsadar Rayuwa, Gwamnatin Legas Ta Kwace Motoci Kimanin 40

Ana Fama da Tsadar Rayuwa, Gwamnatin Legas Ta Kwace Motoci Kimanin 40

  • Gwamnatin jihar Legas ta kai samame kan masu ajiye abubuwan hawa ba bisa ka'ida ba a wasu wurare a faɗin jihar
  • A yayin samamen, jami'an gwamnatin sun sanar da cafke motocin hawa daban-daban wanda sun kai kimanin 40
  • Hukumar kula da zirga zirgar abubuwan hawa ta jihar Legas (LATSMA) ce ta sanar da haka a yau Juma'a, 21 ga watan Yuni 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Hukumar mai kula da zirga zirgar abubuwan hawa a jihar Legas (LASTMA) ta kai samame wuraren ajiye motoci a jihar.

A safiyar yau Jumu'a ne hukumar LASTMA ta kai samamen inda ta kama motoci da yawansu ya kai 40.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun kashe jami'in tsaro

LASTMA
Gwamnati ta kama motocin hawa a Legas saboda kawo cunkoso. Hoto: @followlastma
Asali: Twitter

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da hukumar LASTMA ta wallafa a shafinta na X a safiyar yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar LASTMA ta koma motoci

A yayin samamen da hukumar LASTMA ta kai ta kama motoci 40 da aka ajiyesu a wuraren da sun saɓawa dokar jihar.

Hukumar ta bayyana cewa daga cikin motocin 40, 25 motocin haya ne sai kuma 15 na masu hawa domin bukatar yau da kullum.

Dalilin kama motoci a Legas

Hukumar LASTMA ta bayyana cewa ta kama motocin ne saboda suna kawo cinkoso a fadin jihar wanda yana takura masu abubuwan hawa da masu tafiyar kafa.

LASTMA ta kara da cewa wannan na cikin kokarinta na kawo gyara a birnin Legas da kuma tabbatar da doka da oda.

Wuraren da LASTMA ta kama motoci

A cikin bayanan da hukumar LASTMA ta fitar ta bayyana cewa ta kama motocin ne a yankunan Oyingbo, Ijora da Idumota.

Kara karanta wannan

CNG: Gwamnati ta bayyana abin da ya jawo wata mota mai amfani da gas ta fashe

Jami'in hukumar mai suna Kayode Odunuga ya ce sun kai samamen ne karkashin jagorancin mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin zirga zirga, Sola Giwa.

Direba ya kashe mata Legas

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mata su biyu sun rasa rayuwarsu yayin da su ke aikin sharar titi a jihar Legas da sanyin safiya.

Matan sun rasa ransu ne bayan wani direba ya haura ta kansu inda ya kashe su har lahira a kokarin gujewa kamun jami'an LASTMA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng