NDLEA Ta Kama Dilolin Kwaya Sama da 1,000, Ta Bayyana Kalubalen da Take Fuskanta

NDLEA Ta Kama Dilolin Kwaya Sama da 1,000, Ta Bayyana Kalubalen da Take Fuskanta

  • Hukuma mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana nasarorin da ta samu cikin shekara daya a Katsina
  • NDLEA ta yi nasarar cafke dilolin kwaya da masu safarar ta zuwa kasashen ketare da dama cikin wannar shekarar
  • Shugaban hukumar a jihar Katsina, Hassan Abubakar ne ya bayyana nasorin ga manema labarai a ranar Alhamis

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Hukuma mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar Katsina ta fitar da rahoto kan nasarorin da ta samu.

Hukumar NDLEA ta fitar da rahoton ne domin bayyana yadda ta yi yaki da miyagun kwayoyi a cikin shekara daya.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Buba Marwa
Hukumar NDLEA ta kama dilolin kwaya tare da dauresu a jihar Katsina. Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta fitar da bayanan ne yayin bikin ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dilolin kwaya da hukumar NDLEA ta kama

Kwamandan hukumar NDLEA a jihar Katsina, Hassan Abubakar ya ce cikin shekara daya sun kama diloli masu safarar kwaya 1,344 a jihar.

Hassan Abubakar ya kuma tabbatar da cewa sun kama kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 1,319.258 a jihar.

Sauran nasarorin NDLEA a jihar Katsina

Hukumar ta tabbatar da nasarar wayar da kai ga mutane sama da 56,000 a kan harkar sha da safarar miyagun kwayoyi a cikin shekarar.

A ɓangaren shari'a kuma hukumar ta ce ta samu nasarar gurfanarwa da tabbatar da laifi ga mutane 107 tare da fara shari'a ga mutane 120, rahoton Channels Television.

Kara karanta wannan

"Siddabarun siyasa ne": Na hannun daman Atiku ya fadi dalilin ziyartar Buhari

Kalubalen da NDLEA ke fuskanta

Kwamandan hukumar ya kuma bayyana cewa babban kalunale da suke fuskanta shi ne katsalandan da wasu al'ummar jihar ke yi ga jami'ansu yayin da suka yi kokarin kama masu laifi.

Ya kuma kara da cewa yawaitar yunkurin shigo da kwayoyi jihar duk da kokarin da suke yi yana daga cikin matsalolin da suke fuskanta.

Kotu ta ki sauraron Abba Kyari

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da buƙatar sake neman sabon beli da Abba Kyari ya yi a gabanta.

Alƙalin kotun wanda ya yanke hukuncin ya bayyana cewa buƙatar neman belin da dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sandan ya yi ba ta cancanta ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng