Auren Jinsi: Dan Majalisar Kano Na Neman Najeriya Ta Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Samoa

Auren Jinsi: Dan Majalisar Kano Na Neman Najeriya Ta Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Samoa

  • Dan majalisar da ke wakiltar Takai/Sumaila, Hon. Rabiu Yusuf, ya ce Najeriya za ta iya rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa
  • Tun bayan gabatar da Yarjejeniyar Samo take shan suka saboda ana fargabar ta amince da kuma ba da kariya ga masu auren jinsi
  • Sai dai dan majalisar ya yi nuni da cewa yarjejeniyar na da fa'ida ga Najeriya, don haka akwai bukatar kafa sharudda na yarda da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai a Kano, Rabiu Yusuf ya ce Najeriya na iya amincewa da sassa masu kyau na yarjejeniyar Samoa.

Hon. Yusuf ya ce yarjejeniyar ta kasance abu mai wahala da za a iya tattaunawa a kai saboda tana kunshe da wani bangare na mutunta 'yancin auren jinsi.

Kara karanta wannan

El Rufai ya karɓi baƙuncin Kwankwaso kwanaki bayan kai wa Buhari ziyara a Daura

Dan majalisar Kano ya yi magana kan yarjejeniyar Samoa
Auren Jinsi: Hon. Rabiu Yusuf na neman Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: @sanitijdandago/X, Olena Malik/Getty
Asali: Getty Images

Abin da yarjejeniyar Samoa ta kunsa

Jaridar The Cable ta ruwaito yarjejeniyar Samoa wani babban tsarin doka ne na karfafa dangantaka tsakanin kasashen kungiyar Afirka, Caribbean, da Pacific (OACPS) da kuma Tarayyar Turai (EU).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasashen da ke cikin yarjejeniyar sun hada da kasashen Afirka 47, ciki har da Najeriya, 16 daga yankin Caribbean, kasashe 15 na Pacific, da kuma Jamhuriyar Maldives.

An yi imanin cewa yarjejeniyar Samoa tana goyon baya da kuma kare haƙƙin 'yan luwadi, 'yan madigo, masu canza jinsi, da sauran halayen jima'i da ba na al'ada ba, rahoton BusinessDay.

Samoa: Yarjejeniyar mutunta auren jinsi

Sai dai Najeriya ta fice daga taron rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan Nuwambar bara.

Idan za a tuna, hakan ya faru bayan da wasu kungiyoyin farar hula suka nuna damuwa game da sashe na tara na yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu kwangila daga Saudiya, za a riƙa fitar da nama da waken soya

Ra'ayin 'dan majalisar Kano a kan Samoa

Hon. Yusuf ya bayyana ra'ayinsa dangane da yarjejeniyar Samoa a ranar Alhamis yayin wani taron yanar gizo da cibiyar habaka aikin jarida (CJID).

Dan majalisar wakilan ya lura cewa yarjejeniyar Samoa tana da fa'ida ga Najeriya, don haka akwai bukatar a dauki kasadar amincewa da ita amma a kafa sharadi.

A cewarsa, sharadin da ya kamata a kafa shi ne cire sashe na 9 a yarjejeniyar ta Samoa, tunda sashen ne ke bayyana goyon bayan auren jinsi, wanda kuma ya saba da al'ada da addinin 'yan Najeriya.

"Har yanzu Sanusi II ne Sarki" - Gwamnan kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke game da shari'ar dokar rusa masarautun jihar.

Kwanishinan shari'a na Kano, Barista Haruna Isah Dederi ya ce har yanzu Muhammadu Sanusi II ne sarki bisa ga bayanin wannan hukunci na kotun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel