Riba Biyu: Za a Mayarwa Alhazan Jihar Kaduna Kudi, Wasu Za Su Samu Canjin $50

Riba Biyu: Za a Mayarwa Alhazan Jihar Kaduna Kudi, Wasu Za Su Samu Canjin $50

  • Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yi albishir ga alhazanta na bana da cewa za a biya su wani kaso na kudin hadayar da suka biya a kasa mai tsarki
  • Shugaban kwamitin hadaya na hukumar, Muhammad Dabo ya shaida cewa alhazai 700 za su samu $50 daga kudin da suka bayar a yi masu yanka
  • AVM Muhammad Dabo ya bayyana cewa za a mayar masu da kudin ne biyo bayan ragin kudin rago da kamfanin da ya yi aikin yanka masu ragunan ya yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna - Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na mayarwa da alhazan jihar da suka biya kudin aikin hajjin bana ta hukumar wani kaso na kudin layyarsu.

Kara karanta wannan

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar rayuka 900, musulmai na cigiyar 'yan uwansu

Shugaban kwamitin hadaya na hukumar, AVM Muhammad Dabo mai ritaya da ya bayyana haka, ya ce za a bayar da $50 ga alhazai 700 da suka kamala aikin hajjin bana.

Kaduna
Za a mayarwa alhazan Kaduna wani kaso na kudin layyarsu Hoto: The Kaduna Governor/Inside Haramain
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa hukumar ta dauki mayar da kudin ne saboda an samu ragi daga kamfanin da ya yanka dabbobin layyarsu a Saudiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kowane Alhajin Kaduna zai samu kudin?”

Shugaban kwamitin hadaya na hukumar jin dadin alhazan jihar Kaduna, AVM Muhammad Dabo mai ritaya ya ce alhazai 700 cikin 1,357 za a bawa wani kaso na kudin yankansu.

Rahotanni sun ce gudun ka da su damfari mahajjatan ya sa aka nemi kamfanin da zai taimaka wajen hadayar alhazan saboda muhimmancinsa ga cikar ibadar hajji.

AVM Muhammad Dabo mai ritaya ya ce kamfanin farko da su ka tuntuba ya nemi N200,000 kudin hadayar, daga baya aka samu wani da yanka kowane rago kan riyal 375, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa..

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

NAHCON ta haramta dauko zam-zam

A wani labarin kun ji cewa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta umarci musulmin Najeriya da ka da su dauko ruwan zam-zam daga kasa mai tsarki. Shugaban kula da jigila na hukumar, Muhammad Sanda ne ya bayar da umarnin a Makkah yayin da ake shirye-shiryen dawowar alhazan Najeriya gida bayan sauke farali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.