'Yan Sanda Sun Yi Magana Yayin da Kotu Ke Shirin Sanar da Halataccen Sarkin Kano
- Yayin da ake dakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin sarauta, rundunar ƴan sanda ta buƙaci al'ummar jihar Kano su zauna lafiya
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa ya ce za a tura ƙarin jami'an tsaro domin tabbatar da doka da oda
- A yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 kotun za ta yanke hukunci kan sahihancin dokar rusa masarautu da mayar da Sanusi II
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babban Kotun Tarayya kan rigimar sarauta.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Abdullahi Kiyawa ya nanata kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ƴan sandan ya kuma gargadi duk wani mai yunkurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin kotu ya gaggauta canza tunani.
Kano: Wani mataki ƴan sanda suka ɗauka?
"Tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro, rundunar ƴan sanda za ta tabbatar da dokar haramta zanga-zanga da wasu tarurruka da gwamnatin Kano ta yi."
"Duk wanda ya yi kunnen ƙashi zai ɗanɗana kuɗarsa domin za a girke ƙarin dakarun tsaro da za su tabbatar da bin doka da oda.
"Muna kira ga al'umma su ba jami'an tsaro haɗin kai kuma su taimaka mana da sahihan bayanai don mu gudanar da aikinmu na tabbatar da zaman lafiya."
- Abdullahi Kiyawa.
Rundunar ƴan sandan ta kuma shawarci sauran jami'an tsaron da ba na gwamnati ba kamar ƴan banga da mafarauta su guji shiga harkokin tsaro.
Wannan dai na zuwa ne yayin da Babbar Kotun Tarayya ke shirin yanke hukunci kan sahihancin dokar rushe masarautun Kano da dawo da Muhammadu Sanusi II, rahoton Leadership.
Ɗan Kwankwasiyya ya faɗi halin da suke ciki
Wani ɗan Kwankwasiyya, Sanusi Isiyaku ya shaidawa Legit Hausa cewa babu abin da ke faruwa na tashin hankali a Kano kan batun sarauta.
Sanusi ya ce kowa na ci gaba da harkokinsa kamar kullum bayan wayewar gari, wasu ma ba su san yau za a yanke wani hukunci a kotu ba.
"Lafiya kalau muke zaune, wasu ma ba su san meke faruwa a kotu ba, duk wanda ya tayar da zaune tsaye ɗan can ɓangaren ne kuma su dama haka suke so.
"Muna fatan jami'an tsaro za su ɗauki matakin da ya dace duk da mun ga bangaren da suke goyon baya, Allah ya ci gaba da kare Kano daga masu ƙulla makirci," in ji shi.
Majalisar Kano ta ɗaukaka ƙara
A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Kano ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara kan rigimar sarautar da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinyewa a jihar.
Majalisar ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da shari'ar da Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi ya shigar gaban babban kotun tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng