Rashin Tsaro: Gwamna Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Kamfanin Hako Ma’adanai

Rashin Tsaro: Gwamna Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Kamfanin Hako Ma’adanai

  • Gwamnatin jihar Nasarawa ta cigaba da ɗaukan matakai kan masu hako ma'adanai a jihar domin tabbatar da ingancin tsaro
  • Biyo bayan haka, gwamantin ta dauki matakin gaggawa kan kamfanin Trimadix Geomin Consult Limited da ke aiki a jihar Nasarawa
  • Dama a baya an fara samun takun saka tsakanin kamfanin da gwamnatin jihar inda kamfanin ya zargi gwamnatin da ba daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki mataki kan wani kamfani mai hako ma'adanai a jihar domin inganta tsaro da zaman lafiya.

Kwamishinan muhalli da ma'adanai na jihar, Kwanta Yakubu ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamna a Arewa ya kafa kwamitin kayyade farashin kaya

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamnatin Nasarawa ta rufe kamfanin hako ma'adanai. Hoto: Abdullahi Sule
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin ne biyo bayan korafi da ta samu daga al'umma kan kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rufe kamfani ma'adanai a Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa ta sanar da rufe kamfanin hako ma'adanai na Tridimadix Geomin Consult da ke aiki a yankin Amba a karamar hukumar Kokona.

Gwamnatin ta ce ta samu korafi ne daga sarkin yankin kan yadda kamfanin ke zama barazana ga tsaro da zaman lafiyar al'umma.

Kamfanin ma'adanai ya saɓa doka

Kwamishinan muhalli da ma'adanai na jihar, Kwanta Yakubu ya ce an samu kamfanin da saba dokar jihar, rahoton PM News.

Kwanta Yakubu ya ce kamfanin ya saba dokar hakar ma'adanai da gwamna Abdullahi Sule ya sakawa hannu a shekarar 2022.

"Zaman lafiya shi ne komai" - Gwamnatin Nasarwa

Har ila yau, kwamishinan ya ce sun dauki matakin ne saboda kawo zaman lafiya da cigaban al'umma shi ne babban abu da suka sa a gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin za ta cigaba da bibiyan masu hakar ma'adanai da suka saɓa doka domin daukan mataki a kansu.

Ramin ma'adanai ya rufta a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa an kara samun ruftawar ramin ma'adanai da mutane a jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru ne bayan mutane sama da 20 sun mutu a wani ramin a jihar, shugaban hukumar NSEMA ya yi karin haske kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng