An rufe wurin hakar ma'adanai na jihar Kano

An rufe wurin hakar ma'adanai na jihar Kano

- Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta bi umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe wurin hakar ma'adanai

- A jiya ne hukumar ta rufe wurin hakar ma'adanan da ke karamar Sumaila, kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta

A jiya Talata ne hukumar 'yan sandan jihar Kano ta rufe wurin hakar ma'adanai da ke Rimi, cikin karamar hukumar Sumaila, domin tabbatar da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar.

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe kowanne wurin hakar ma'adanai dake kasar nan, saboda wasu dalilai na matsalar tsaro.

An rufe wurin hakar ma'adanai na jihar Kano
An rufe wurin hakar ma'adanai na jihar Kano
Asali: UGC

A wata sanarwa da jami'in hukumar ya fitar, DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro masu yawa zuwa wurin da ake hakar ma'adanan, domin bin umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar.

A sanarwar da DSP Haruna ya sanyawa hannu ya bayyana cewa "A jiya Talata 9/4/2019 hukumar 'yan sanda ta jihar Kano ta tura da jami'anta su ziyarci wurin hakar ma'adanan domin tabbatar da cewa mutanen yankin sun bi doka."

KU KARANTA: Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

Bayan haka kuma DSP Haruna ya bukaci al'umma da su yi hakuri su bi doka har zuwa lokacin da gwamnati za ta bude wurin.

Idan ba a manta ba a satin da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe duk wasu wuraren da ake hakar ma'adanai a wasu jihohi a kasar nan, hakan ya biyo bayan wasu bayanan sirri da gwamnatin tarayyar ta ke samu na kashe-kashen da ake fama da shi a yankunan jihar Zamfara, Katsina, Kaduna da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel