Wani Alhaji Ya Fito da Ƙimar Najeriya a Lokacin da Ya Tsinci Maƙudan Daloli a Madinah

Wani Alhaji Ya Fito da Ƙimar Najeriya a Lokacin da Ya Tsinci Maƙudan Daloli a Madinah

  • Wani mahajjaci daga jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ya nuna kyakkyawan hali yayin da ya tsinci jakar hannu ɗauke da maƙudan kudi a Madinah
  • Alhaji Abba Saadu Limawa ya yi cigiya domin bai wa mai jakar kayansa amma ba a ga mai ita ba, don haka ya kai wa hukumar NAHCON
  • Shugaban hukumar alhazai ta Jigawa, Ahmad Umar Labo ya ce tsintuwar ta biyo ta hannunsa kafin a miƙawa shugaban NAHCON a taron kammala Arafah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Wani Alhaji daga jihar Jigawa ya mayar da jakar hannu da ya tsinta a Masallacin Annabi SAW da ke Madina a ƙasar Saudiyya.

Duk da jakar na ɗauke da Dalar Amurka 800, kimanin N1,185,000 a kudin Najeriya, Alhajin ya mayar da ita ga hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa NAHCON a Makkah.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta ba Alhazan Najeriya umarni yayin da suke shirin dawowa gida

Alhazai a filin Arafah.
Alhaji daga Jigawa ya mayar da jakar da ya tsinta a Madinah Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Bayan Dalolin Amurka, jakar da alhajin ya tsinta na ɗauka da Riyal 690 da wasu kuɗaɗen ƙasar Rasha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhajin Naeriya ya tsinci dalolin kudi

Alhajin mai suna, Abba Saadu Limawa ya fito ne daga kauyen Limawa a ƙaramar hukumar Dutse ta jihar Jigawa, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Ya mayar da jakar domin a yi cigiya ga shugaban NAHCON na ƙasa, Malam Jalal Ahmad Arabi a wurin taron da aka shirya bayan kammala tsayuwar Arafah a Makkah.

Yadda lamarin ya faru tun a Madinah

Ahmad Umar Labo, shugaban hukumar jin daɗin alhazai na Jigawa ya tabbatar da wannan hali nagari da alhajin ya nuna a wata sanarwa.

Ya ce Alhaji Abba Sa'adu ya yi cigiyar jakar na tsawon kwanaki biyu a Masallacin Annabi SAW amma ba a samu mai ita ba, rahoton Platform Times.

Kara karanta wannan

Sallah: Atiku ya kai ziyara ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, hotuna sun bayyana

Ahmad ya ƙara cewa bayan rashin samun mai jakar, mutum ya tuntuɓi shugabansu na Jigawa wanda shi kuma ya sanar da hukumar NAHCON.

Daga ƙarshe dai Alhajin ya bai wa hukumar jakar ɗauke da kuɗafen da ƴa tsinta ba tare da ya taɓa ko kwandala ba domin a ci gaba da cigiya.

Abubuwan da huɗubar Arafah ta kunsa

A wani rahoton na daban miliyoyin mahajjata daga ƙasashen daban-daban suka gabatar suka yi tsayuwar Arafa a kasa mai tsarki a lokacin hajjin bana.

Hawan Arafa yana daya daga cikin manyan ayyukan Hajji da ake bukatar mahajjata maza da mata su gudanar yayin aikin Hajji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel