Murna Ta Koma Ciki, 'Yan bindiga Sun Hallaka Amarya Mako 1 Tak Bayan Ɗaura Aurenta

Murna Ta Koma Ciki, 'Yan bindiga Sun Hallaka Amarya Mako 1 Tak Bayan Ɗaura Aurenta

  • Maharan sun yi ajalin amarya mako ɗaya da ɗaura mata aure gabanin ta tare gidan mijinta a jihar Anambra ranar Litinin
  • Lamarin ya faru ne yayin da ƴan bindiga masu tilasta bin dokar zaman gida suka kai farmaki kauyuka biyu, inda suka kashe mutane da yawa
  • A halin yanzu dai rundunar ƴan sanda da jami'an ƴan banga sun fara farautar maharan da nufin kamo su a gurfanar da su a gaban shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Amarya da ba ta wuce mako ɗaya da shiga daga ciki ba na cikin waɗanda ƴan bindiga suka kashe a harin Nnobi da ke jihar Anambra.

Rahotanni daga bakin iyalanta sun nuna cewa amaryar tana jiran dawowar mijinta daga ƙasar waje sannan ta tare, bisa tsautsayi harsashi ya same ta a harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 6 yayin wani hari a Kaduna

Yan sandan Najeriya.
Mahara sun yi ajalin amarya mako ɗaya da ɗaura mata aure a Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wata majiya daga iyalan marigayyar ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Punch ranar Talata amma ba a bayyana sunan amaryar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Tun farko dai wasu ƴan bindiga sun kai farmaki garuruwan Nnewi da ke ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa da Nnobi a ƙaramar hukumar Idemili, jihar Anambra ranar Litinin.

Maharan sun kashe mutanen da har yanzun ba a tantance adadinsu ba ciki har da ƴan banga, sun kuma jikkata wasu da dama, cewar rahoton The Cable.

Lamarin ya haifar da firgici a garuruwan biyu yayin da ‘yan kasuwa da mazauna garin suka ruga a cikin gida domin tsira daga sharrin maharan.

Sai dai duk da haka ƴan bindigar waɗanda ake kyautata zaton masu kaƙaba dokar zaman gida ne, sun buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

Amarya ta rasa ranta a harin Anambra

Majiyar ta ce:

“Daga cikin wadanda aka kashe jiya (Litinin) a Nnobi akwai ƴar uwata, sati ɗaya kenan da ɗaura aurenta. Tana jiran mijinta ya dawo daga kasar waje ne kafin ta tare.
"Matashiya ce ƴar shekara 22 a duniya kuma ita ce ɗiya ɗaya tilo a wurin iyayenta. Lamarin akwai ban tausayi kuma ba karamar illa ya yi mana ba."

An tattaro cewa tuni dakarun ƴan sanda da ƴan banga suka bazama domin farautar maharan da nufin kamo su doka ta yi aiki a kansu.

Ƴan bindiga sun kai hari Kaduna

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kashe mutane yayin da suke tsaka da taro a kauyen Ewehko, ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige akalla mutum biyar har lahira ido na ganin ido ranar Litinin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262