Rigimar Masarautar Kano: Babban Lauya Ya Fito da Kuskuren Kotun da Ta Ba Bayero Nasara

Rigimar Masarautar Kano: Babban Lauya Ya Fito da Kuskuren Kotun da Ta Ba Bayero Nasara

  • Babban lauya, Femi Falana ya fito da kuskuren babbar kotun tarayya game da hukuncin da ta yanke kan shari'ar masarautar Kano
  • Femi Falana ya tunatar da babbar kotun tarayya da ma kotun masana'antu cewa ba su da hurumin sauraron shari'ar masarauta
  • A cewar lauyan, hukuncin da kotu ya yanke na ba Aminu Ado Bayero nasara ya yi hannun riga da wasu sashe na kundin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Babban lauyan Najeria, Femi Falana, ya tunatar da babbar kotun tarayya da kotun masana’antu ta kasa cewa ba su da hurumin shiga al’amuran da suka shafi sarauta a kasar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Falana ya tunatar da alkalai da lauyoyi cewa rigingimun sarauta suna karkashin hurumin babbar kotun jiha ne.

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

Femi Falana ya yi magana kan rigimar masarautar Kano
Femi Falana ya tunatar da babbar kotun tarayya huruminta a rigimar masarautar Kano @SanusiSnippets, @HRHBayero
Asali: Twitter

Kotu ta ba Aminu Bayero nasara

Jaridar Vanguard ta ruwaito Falana na mayar da martani ne kan rigimar da aka yi tsakanin sarki Ado Bayero da Sarki Sanusi Lamido Sanusi a kan kujerar Sarkin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mun ruwaito wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta umurci gwamnatin Kano da ta biya Naira miliyan 10 a matsayin diyyar tauye hakkin Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero.

Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Aminu Bayero ya shigar na neman a bi masa hakkinsa na dan adam.

Falana ya kalubalanci nasarar Aminu Ado Bayero

Amma Femi Falana, a cikin sanarwar ya kalubalanci babbar kotun tarayyar kan yanke wannan hukunci alhalin ta san ba ta da hurumi a kai, in ji rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka

Barista Falana ya bayyana hukuncin kotun a matsayin, "kuskure babba" domin ba za a iya tabbatar da shi ba a karkashin sashe na 251 da 254 (C) na kundin tsarin mulkin kasar.

Haka zalika, babban lauyan ya bayyana cewa batun sarauta ba lamari ne da ya shafi 'hakkin dan adam' ba kuma kotun ba za ta iya aiwatar da shi a karkashin tanadin sashe na 31 na kundin tsarin mulkin kasar ba.

Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ta rigamu gidan gaskiya tana da shekaru 88 a duniya.

An ce Cif Misis Florence Morenike Saraki ta rasu ne a ranar Talata, 18 ga watan Yunin 2024 bayan an garzaya da ita wani asibitin Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel