Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Rikicin Masarautar Kano

Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Rikicin Masarautar Kano

  • Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce ta samu umarnin kotu guda biyar dangane da rikicin masarautar jihar da yaƙi ci ya ƙi cinyewa
  • Rundunar ƴan sandan ta ce tuni ta miƙa umarnin kotun ga Antoni Janar kuma ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi
  • CP Usaini Gumel ya bayyana cewa jami'ansa za su kare magoya bayan Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, da kuma mazauna Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kano, jihar Kano - Usaini Gumel, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, ya yi magana kan umarnin kotu da suka samu kan rikicin masarautar Kano.

Kwamishinan ya bayyana cewa sun miƙa umarnin kotu guda biyar da suka samu zuwa ga ministan shari'a, Lateef Fagbemi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ido na ganin ido, sun kashe bayin Allah ranar yawon Sallah

'Yan sanda sun samu umarni kan rikicin masarautar Kano
Kotu ta ba 'yan sanda umarni biyar kan rikicin masarautar Kano Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Wane umarni ƴan sanda suka samu a Kano?

Majiyar Legit.ng ta ce a wata hira da aka yi da kwamishinan ƴan sandan wacce aka buga a ranar Talata, 18 ga watan Yuni, Usaini Gumel ya bayyana cewa ƴan sanda a yanzu suna jiran umarnin ministan shari'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun karɓi umarnin kotu kusan biyar kuma muka mika su ga Antoni Janar na tarayya (AGF) kuma ministan shari’a. Muna jiran martaninsa da umarninsa."
"Kuma yayin da muke jiran abin da zai faru a kotu ko umarni daga AGF, dole ne mu kare sarakunan biyu da ke rikici."
"Dole ne mu kare magoya bayan sarakunan biyu da kuma mazauna jihar."

- Usaini Gumel

Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu

Idan dai ba a manta ba tsohon gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha alwashin cewa ba za su amince da dokar ta ɓaci a jihar ba.

Kara karanta wannan

"Ka yafewa maƙiya," Matasan Arewa sun aike da saƙo ga Sarki Aminu Ado Bayero

Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya wacce Bola Tinubu ke jagoranta da yi wa tsaron Kano zagon ƙasa sakamakon ƙin janye manyan jami’an da ke gadin Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Batun cafke Aminu Ado Bayero

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya fayyace musabbabin ba da umarnin kama Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da ya yi bayan ya tuɓe shi daga sarauta.

Gwamna Abba Kabir ya ce ya ba da umarnin ne bayan Sarki Aminu Ado Bayero ya dawo Kano da neman tayar da zaune tsaye a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel