"Ba Ku Kadai Ba Ne": Tinubu Ya Magantu Kan Talauci a Kasa, Ya Kawo Mafita

"Ba Ku Kadai Ba Ne": Tinubu Ya Magantu Kan Talauci a Kasa, Ya Kawo Mafita

  • Shugaban ƙasa Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayanin cewa matsalar talauci ba ƴan Najeriya kaɗai ta shafa ba
  • Shugaba Tinubu ya bayyana cewa akwai talauci da wahala a ƙasar nan amma hakan matsala ce wacce ta shafi dukkanin duniya ba Najeriya kaɗai ba
  • Ya yi nuno da cewa dole ne a magance matsalar ayyukan ƴan bindiga da ta'addanci domin manoma su samu damar noma abinci a gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba ƴan Najeriya ne kaɗai ke fuskantar talauci a duniya ba.

Shugaban ƙasan wanda ya amince cewa akwai talauci da wahala a ƙasar nan, ya ce dole ne a magance ƙalubalen.

Kara karanta wannan

Sallah: Sarkin Musulmi ya yi muhimmiyar tunatarwa ga shugabanni

Tinubu ya magantu kan talauci a Najeriya
Tinubu ya ce ba Najeriya kadai ke fama da talauci ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ya yi bayanin cewa ɗaga cikin hanyoyin magance ƙalubalen ita ce kawar da ƴan bindiga da ƴan ta'adda ta yadda manoma za su iya komawa gona.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya gana da ƴan majalisa

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƴan majalisar tarayya, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Tawagar ta samu jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mataimakinsa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu da sauransu, rahoton The Punch ya tabbatar.

Me Tinubu ya ce kan talauci a Najeriya

"Eh akwai talauci, ana shan wuya a ƙasar nan. Ba mu kaɗai ba ne ke fuskantar hakan, amma dole ne mu fuskanci ƙalubalenmu."
"Dole ne mu samo hanyar da za mu kawar da ayyukan ƴan bindiga da ta'addanci ta yadda manoma za su iya noma abinci a gonakinsu."

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya kan Bola Tinubu

"Idan babu hanyoyi masu kyau da za a kawo abincin ga jama'a, ko da an noma abincin amma ana yin asarar kaso 60-70%, za a samu babbar matsala."

- Bola Tinubu

Tinubu ya tafi ƙasar waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afirika ta Kudu a ranar Talata, 18 ga watan Yunin 2024.

Shugaban ƙasan ya bar birnin Legas ne da misalin ƙarfe 11:06 na safe a ranar Talata, 18 ga watan Yuni domin zuwa ƙasar ta Afirika ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng