Dubun Kasurgumin Dan Ta’adda Ya Cika a Yobe, ’Yan Sanda Sun Bayyana Abin da Ya Aikata

Dubun Kasurgumin Dan Ta’adda Ya Cika a Yobe, ’Yan Sanda Sun Bayyana Abin da Ya Aikata

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta sanar da nasarar cafke kasurgumin ɗan ta'adda da ya fitini mutane, Haruna Muhammad a jihar
  • Rahoto ya nuna cewa an kama Haruna Muhammad ne a kauyen Nangillam dake karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe
  • Kakakin 'yan sanda a jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya bayyana irin laifuffukan da ake zargin dan ta'addan da aikatawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta yi nasarar kama daya daga cikin shugabannin 'yan ta'adda a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

DAn ta'adda
Yan sanda sun kama dan ta'adda a jihar Yobe. Hoto: Dungus Abdulkarim
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da Dungus Abdulkarim ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laifin da dan ta'addan ya aikata

Kakakin 'yan sanda ya ce ana zargin Haruna da aikata laifuffuka da dama ciki har da kiran waya yana neman kudi da barazanar kisa.

Dungus Abdulkarim ya ce ɗan ta'addan ya shahara da shiga ƙauyuka da wasu jihohin yana barazana ga mutane.

Wani mazaunin kauyen Siminti dake garin Lantewa a karamar hukumar Tarmuwa ya ce ɗan ta'addan ya yi barazanar kashe shi.

Mutumin ya ce Haruna Muhammad ya bukaci ya tura masa kudi Naira miliyan 3 ko kuma ya kashe shi tare da iyalansa.

Dan ta'addan ya amsa laifi

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa Haruna Muhammad ya amince da laifinsa kuma ya ambaci wasu da suke aikata ta'addanci tare.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Kwamishinan yan sandan jihar ya ce zasu cigaba da farautar yan ta'adda har sai sun ga bayansu ya kuma bukaci mutane da su gaggauta sanar dasu duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Najeriya ta nemi tallafi daga EU

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi kira ga kungiyar tarayyar Turai da ta tallafawa Nigeria a yaki da matsalar rashin tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Badaru, ya nuna damuwa kan yadda kasashen Africa ke fama da rashin tsaro a yayin da kuma suke fama da talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng