Babban Sallah: An Sace Ragon Layyan Babban Limami a Arewacin Najeriya
- Wasu ɓata gari sun sace ragon layya na babban Limamin kauyen Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato
- Limamin da ya yi limancin Sallar idi a garin, Malam Haruna Yakub ne ya bayyana haka a cikin huɗuba bayan sallame Sallah raka'a biyu ranar Lahadi
- Malam Haruna ya nuna damuwarsa da mamakin yadda mutane suka lalace, inda ya tunatar da cewa za a yi kowa hisabi ranar lahira
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Wasu ɓarayi sun sace ragon layya na babban limamin Masallacin garin Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Ɓata garin sun ɗauke ragon ne yayin da ake tsaka da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a daren ranar jajibirin Babbar Sallah a gidan limamin.
Malam Haruna Yaqub, wani malamin Addinin Musulunci ne ya bayyana haka a cikin huɗubar da ya yi bayan kammala raka'o'i biyu na Sallar Idi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sacewa Liman ragon sallah
Limamin ya yi Alla-wadai da sace ragon layyar babban Malaminsu, yana kai bayyana lamarin da muguwar ɗabi'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"Jiya daddare aka sace ragon da babban Limaminmu ya sayo domin ya yi layya, lamarin ya tada mana hankali, mun yi mamakin sace ragon Liman.
"Wannan na nufin mutane ba su jin tsoron Allah, yanzu mun yi lalacewar da mutane za su sace ragon da aka saya domin yin ibadar addini,"
- Malam Yakub.
Limamin ya tunawa mutane hisabi
Malam Haruna ya kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah, su daina sata ko aikata wasu miyagun laifuka, The Nation ta ruwaito.
Ya kuma ja hankalin mutane da tunatar da su cewa Allah SWT zai yi kowa hisabin ayyukansa a ranar gobe ƙiyama.
"Wannan shi ne lokacin da ya dace mutane su tubar ma Allah su koma kan tafarki madaidaici, ya kamata mutane sun daina saɓawa Allah, su maida hankali wajen yin ayyukan alheri."
Matasa sun tada hargitsi kan naɗin sarauta
A wani rahoton kuma matasa sun ɗauki zafi, sun farmaki jami'an gwamnati, ƴan sanda da sojoji a wurin bikin naɗin Sarkin Nkomoro a yankin Ezza ta Arewa a Ebonyi
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne daga lokacin da wakilin gwamnati ya faɗi sunan wanda za a naɗa a matsayin sabon sarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng