Sojojin Najeriya Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 100 Ana Shagalin Sallah a Arewa

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 100 Ana Shagalin Sallah a Arewa

  • Jirgin yaƙi ya kai samame sansanin ƴan bindiga, ya yi nasarar hallaka aƙalla ƴan ta'adda 100 a yankin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya ce sojojin sun lalata babura sama da 45 da wasu kayan aikin ƴan bindigar
  • Kaula ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar daƙile harin garkuwa da mutane tare da ceto mata uku a Jibia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe ƴan bindiga sama da 100 a wani samame da ta kai sansanin Kuka Shidda da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji ne suka yi ruwan wuta kan ƴan bindigar da daddare, wanda bisa nasara suka murƙushe su da yawa.

Kara karanta wannan

Aiki da cikawa: Ana tsaka da bikin babbar sallah, sojoji sun kashe dan bindigan da ya addabi Kaduna

Jirgin sojojin saman Najeriya.
Jirgin yaƙi ya ragargaji ƴan bindiga a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Sojojin sun kai samamen ne a sansanin kasurgumin ɗan bindiga, Yusuf Yellow da babban yaronsa Rabe Imani, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwammatin Katsina ta tabbatar da haka

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya fitar, ya ce sama da babura 45 aka lalata a yayin harin da jiragen sojojin suka kai.

Ya ce wannan shi ne karo na uku da sojojin saman Najeriya suka samu nasarar kai farmaki da kashe ƴan ta'adda a yankin Faskari-Kankara kwanan nan.

Kaula ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunkurin garkuwa da mutane da safiyar ranar Lahadi a yankin ƙaramar hukumar Jibia.

Ƴan sanda sun ceto mata 3 a Katsina

A ruwayar Daily Post, Kaula ya ce:

"Ƴan sanda sun samu kiran gaggawa kan wani harin garkuwa da mutane da aka kai yankin Kwata a ƙaramar hukumar Jibia da misalin karfe 4:15 na asuba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

"Nan take suka kai ɗauki, inda suka tare hanyar da ƴan bindigar za su wuce, aka yi musayar wuta wanda daga ƙarshe maharan suka arce suka bar mata 3 da suka ɗauƙo,"

- Ibrahim Kaula

Ya ce dakarun ƴan sandan sun ceto Ummulkhari Abubakar (23) Shafa’atu Abubakar (35), da kuma Maryam Lawal (15) cikin ƙoshin lafiya.

Jigirin yaƙi ya samu nasara a Bakori

A wani rahoton kun ji cewa Sojojin saman Najeriya sun mayar da martani, sun kashe tulin ƴan bindiga a jihar Katsina bayan harin da aka kai yankin Ƙankara.

Sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kaula ya ce rahoton bayan samamen sojin ya nuna ƴan bindiga 29 sun bakunci lahira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262