Matasa Sun Fusata, Sun Farmaki Jami'an Gwamnati Kan Rikicin Naɗin Sarauta

Matasa Sun Fusata, Sun Farmaki Jami'an Gwamnati Kan Rikicin Naɗin Sarauta

  • Matasa sun ɗauki zafi, sun farmaki jami'an gwamnati, ƴan sanda da sojoji a wurin bikin naɗin Sarkin Nkomoro a yankin Ezza ta Arewa a Ebonyi
  • Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne daga lokacin da wakilin gwamnati ya faɗi sunan wanda za a naɗa a matsayin sabon sarki
  • Mazaunan sun nuna rashin amincewarsu da kokarin gwamna na ƙaƙaba masu tsohon kwamishinan INEC, Cif Jacob Nwakpa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Mutane da dama sun tsallake rijiya da baya a kauyen Nkomoro da ke ƙaramar hukumar Ezza ta Arewa a jihar Ebonyi sakamakon faɗan da ya kaure.

Rikici ya kaure ne a garin a wurin naɗin sarautar basaraken Nokomoro, inda mutanen garin suka tada hargitsi a tsakaninsu kan wanda aka naɗa masu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Taswirar jihar Ebonyi.
Matasa sun farmaki jami'an tsaro da alkali kan rikicin sarauta a jihar Ebonyi
Asali: Original

Waɗanda suka sha da ƙyar daga zuwa shaida naɗin sun haɗa da ƴan sanda, sojoji da wani alƙalin kotun majistire, Amaechi Nwakpa da wasu manyan mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, ƴan jarida da suka haɗa da masu ɗauko rahoton kafar watsa labarai da jihar (EBBC) da Rediyo Najeriya sun tsallake rijiya da baya.

Menene asalin rikicin sarautar?

Bayanai sun nuna cewa mazauna garin sun jima su na faɗa da juna kan rigimar sarauta.

A zanga-zanga daban-daban da koken da suka miƙa wa gwamnatin Ebonyi, mazauna garin suna nuna ba su kaunar tsohon kwamishinan hukumar zaɓe (INEC) da ake neman ƙaƙaba masu.

Mazauna garin sun bayyana damuwa kan tsohon kwamishinan INEC, Cif Jacob Nwakpa da gwamnatin Ebonyi ta naɗa a matsayin Sarki.

Yadda matasa suka yi ɓarna

Wasu fusatattun matasan garin da ba su ƙaunar nadin sarautar Cif Nwakpa ne suka tada hargitsi, inda suka lalata motocin Mista Inya da sojoji da kuma alkalin kotun.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya faɗi wasu gwamnoni da ke amfani da ƴan daba su murɗe zaɓe

Matasan sun kuma farmaki wasu jami’an gwamnati da suka hada da sakatariyar karamar hukumar Ezza ta Arewa, Misis Samuel Nweke da Chika Igboke, suka lalata motocinsu.

An tattaro cewa matasan na dauke da makamai da suka hada da sanduna, duwatsu da sauran abubuwa masu hadari, cewar rahoton Daily Post.

Rikicin ya fara ne a lokacin da Mista Chika Igboke, jagoran cibiyar ci gaban Imoha, ya karanta wasika daga ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu na umarnin nadin Cif Nwakpa.

Wasu daga cikin al’ummar yankin sun nuna rashin amincewarsu da wannan wasikar inda suka dage cewa ba zai yiwu gwamnatin jihar ta ƙaƙaɓa musu Cif Nwakpa ba.

Saƙon matasan Arewa ana rikicin sarautar Kano

A wani rahoton kuma matasan Arewa sun tura sakon barka da Sallah da nuna goyon baya ga Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar matasan Arewa (AYAF), Nuhu Magaji ya fitar, ya roƙi basaraken ya yafe wa maƙiyansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel