"Ka Yafewa Maƙiya," Matasan Arewa Sun Aike da Sako Ga Sarki Aminu Ado Bayero
- Matasan Arewa sun tura sakon barka da Sallah da nuna goyon baya ga Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
- A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar matasan Arewa (AYAF), Nuhu Magaji ya fitar, ya roƙi basaraken ya yafe wa maƙiyansa
- Ya kuma yi kira ga ɗaukacin mazauna Kano da su rungumi zaman lafiya da ƙaunar juna domin kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ƙungiyar matasan Arewa (AYAF) ta aike saƙon barka da Sallah ga Sarki na 15, Aminu Ado Bayero a jihar Kano.
Matasan sun roƙi basaraken da ya ci gaba da jagorantar al'ummar jihar Kano ba tare da nuna gajiyawa ba kuma ya yafewa waɗanda suka nuna masa ƙiyayya.
Shugaban ƙungiyar AYAF, Nuhu Magaji ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ta barka da Sallah da ya fitar ranar Lahadi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yabawa Sarkin Kano na 15 bisa jajircewarsa wajen ganin an samu hadin kai tsakanin al'umma da kuma ci gaban Kano.
Matasan Arewa sun goyi bayan Sarki Aminu
"A wannan lokacin da Musulmi ke gudanar da bukukuwan babbar Sallah, kungiyar ci gaban matasa ta Arewa (AYAF) na mika sakon Barka da Sallaj ga Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero.
"Duk da taƙaddama da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, muna goyon bayan Sarki Aminu Bayero, wanda ya kasance ginshiƙin zaman lafiya, ci gaba, da kwanciyar hankali.
“Sarkin Aminu ya sadaukar da kansa ga masarauta, kuma abubuwan da ya yi sun zama abin koyi gare mu. Mun fahimci irin namijin kokarin da yake yi na inganta hadin kai, fahimtar juna, da ci gaba a Kano da ƙasa baki ɗaya."
- Nuhu Magaji.
Kungiyar matasan ta kuma yi kira ga ɗaukacin mazauna Kano da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai domin ci gaban jihar, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Kotu za ta raba gardama a shari'ar sarauta
A wani rahoton na daban Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukunci kan sahihancin mayar da Muhammadu Sanusi II kan sarautar Kano.
Kotun ta zaɓi ranar 20 ga watan Yuni, 2024 domin yanke hukunci kanɓhalascin sabuwar dokar masarautar Kano da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng