Sallah: Sarkin Musulmi Ya Yi Muhimmiyar Tunatarwa Ga Shugabanni

Sallah: Sarkin Musulmi Ya Yi Muhimmiyar Tunatarwa Ga Shugabanni

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya tunatar da shugabanni kan halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki
  • Sarkin Musulmin ya buƙaci shugabanni a dukkanin matakai da su zaga damtse wajen ganin sun ceto mutane daga cikin halin tsadar rayuwar da suka samu kansu a ciki
  • Ya yi wannan kiran ne a cikin huɗubar da ya yi ta Sallar Idi a birnin Sokoto a ranar Lahadi, 16 ga watan Yunin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya tunatar da shugabanni kan halin tsadar rayuwa da ake ciki.

Sarkin Musulmin ya yi kira ga shugabannin a dukkanin matakai da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sallah: Buhari ya fadi abin da 'yan Najeriya suka yi da ya faranta masa rai

Sarkin Musulmi ya shawarci shugabanni
Sarkin Musulmi ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana hakan ne a cikin huɗubarsa bayan kammala Sallar Idi a filin Idi na Fakon Idi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya yi kira ga shugabanni

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa Najeriya na fama da tarin matsaloli yayin da mutanen ƙasar nan ke ci gaba da fuskantar ƙuncin rayuwa.

A cewarsa, akwai buƙatar a ƙara ƙaimi domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke ciki.

Ya kuma yi kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tunkarar ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a ƙasar nan, yana mai cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu idan ba tsaro, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Shugabanni su ji tsoron Allah kuma su yi aiki tuƙuru domin biyan buƙatun mutanen da suke shugabanta."

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya kan Bola Tinubu

- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Wace shawara Sarkin Musulmi ya ba da?

Ya shawarci ƴan Nijeriya da su kasance masu son zaman lafiya da kishin ƙasa.

Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da ba da goyon baya da kuma yiwa shugabanni addu'a domin su samu nasara.

Sarkin Musulmi ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya shawarci ƴan Najeriya da su rungumi tarin ƙalubalen da suke fuskanta, sannan su yi ƙoƙarin magance su.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a fadarsa da ke birnin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng