Jigo a APC Ya Nemi Muhimmiyar Bukata Wajen 'Yan Najeriya Kan Bola Tinubu

Jigo a APC Ya Nemi Muhimmiyar Bukata Wajen 'Yan Najeriya Kan Bola Tinubu

  • Sanata Ajibola Basiru ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da sanya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin addu'o'insu
  • Sakataren na jam'iyyar APC na ƙasa ya buƙaci a yi addu'ar ne domin gwamnatin Tinubu ta samu nasara wajen sauke nauyin da ke wuyanta
  • Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da jajircewa da nuna juriya domin a samu al'umma ta gari a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu addu’a.

Ajibola Basiru ya buƙaci a yiwa shugaban ƙasan addu'ar ne domin gwamnatinsa ta samu nasara wajen tafiyar da al’amuran ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sallah: Tinubu ya bayyana abin da Najeriya ke bukata ta samu ci gaba

Jigo a APC ya bukaci a yiwa Tinubu addu'a
Sanata Ajibola Basiru ya bukaci 'yan Najeriya su sa Tinubu cikin addu'a Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Sakataren na APC ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi bayan kammala Sallar Idi a filin Sallar Idi na Osogbo ta Tsakiya da ke Oke Bale, Osogbo, babban birnin Jihar Osun, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake ƙarin haske, Ajibola Basiru ya ce bikin sallar na bana na da matuƙar muhimmanci ta fuskoki da dama, inda daga ciki yace akwai sadaukarwa, tawali’u da kuma biyayya ga umarnin Allah, rahoton The Sun tabbatar.

Wace shawara jigon APC ya ba da?

"Muna kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen nuna taƙawa, riƙon amana, tawali’u wanda hakan zai sanya a samu al'umma ta gari."
"Muna taya ɗaukacin al’ummar Musulmi da ƴan Najeriya murnar zuwan wannan lokacin. Muna kira a gare su da su ci gaba da yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara."

Kara karanta wannan

Albashi: Kungiyar NLC ta juyawa Tinubu baya, ta fadi gaskiyar halin da ake ciki

- Sanata Ajibola Basiru

Manyan tituna a Osogbo, babban birnin jihar Osun, sun kasance babu cunkoso a ranar Lahadi, yayin da al’ummar Musulmi suka gudanar Sallar Idi a filin Idi daban-daban.

Tinubu ya faɗi abin da Najeriya ke buƙata

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana abin da Najeriya take buƙata domin ta samu ci gaban da waɗanda suka kafata suka yi fata.

Shugaban ƙasar ya nuna cewa ƙasar nan na buƙatar ƴan ƙasa masu sadaukarwa domin ta cika wannan mafarkin na waɗanda suka assasata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel