'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Sakatariyar Ƙaramar Hukuma, Sun Tafka Babbar Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Sakatariyar Ƙaramar Hukuma, Sun Tafka Babbar Ɓarna

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Ogbaru, jihar Anambra
  • Bayan bude wuta da ya jefa mutane cikin firgici, 'yan bindigar sun kuma kona motoci hudu na 'yan kungiyar sa kai
  • Rundunar 'yan sandan Anambra ya bayyana matakin da ta dauka da kuma abin da ya biyo bayan wannan farmaki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogbaru, jihar Anambra - Wasu gungun 'yan bindiga sun farmaki sakatariyar karamar hukumar Ogbaru da ke a jihar Anambra.

An ce 'yan bindigar wadanda suka kai harin a safiyar ranar Asabar sun kona motoci hudu da ke ajiye a harabar wajen.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan harin 'yan bindiga a Anambra
'Yan bindiga sun kai farmaki sakatariyar karamar hukumar Anambra.Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Harin 'yan bindiga a sakatariyar Ogbaru

Kara karanta wannan

Mutuwar ɗan sanda ta jawo tashin hankali a Abuja, an ƙona gawar wani ɗan fashi

Duk da cewa babu asarar rai, amma jaridar Premium Times ta ruwaito 'yan bindigar sun yi harbi saman iska domin korar jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce wannan harin ya jefa jama'a cikin tsoro, tunda ya na zuwa ne kwanaki biyu bayan an kashe sojoji biyu da ke tsaron ma'aikatan mai a garin.

Wata majiya ta bayyana cewa:

"A kwanaki biyu baya, 'yan bindiga sun farmaki motar sojoji da ke jigilar ma'aikatan mai, an kashe sojoji biyu, an raunata daya."

Yan sandan Anambra sun yi martani

Rahoton Channels TV ya nuna cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da rahoton kai farmakin.

Tochukwu Ikenga ya ce 'yan bindigar sun kona motoci hudu na kungiyar 'yan sa kai ta jihar da suke yin sintirin tsaro da su a yankin.

Kara karanta wannan

Harajin noma: Ƴan bindiga sun karɓi Naira miliyan 6.2 daga manoman ƙauyukan Kaduna

Jami'an tsaro sun fatattaki 'yan bindigar

Ikenga ya ce:

"Kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra, CP Nnaghe Obono Itam, ya yi Allah wadai da harin sakatariyar Ogbaru.

"Duk da barnar da suka yi, 'yan kungiyar sa kai sun mayar da musayar wuta har zuwa lokacin da 'yan sanda suka isa wajen tare da fatattakar 'yan bindigar."

'Yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki ofishin rundunar 'yan sandan karamar hukumar Abaji, babban birnin tarayya Abuja, kuma har sun kashe jami'i daya.

An kuma ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki wani bankin First Bank da ke kusa da ofishin 'yan sandan inda suka yi awon gaba da kudi masu yawa duk da yin artabu da sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel