Kano: Ba Kamar Aminu Ado Ba, Sanusi II Ya Fadi Abin da Zai Kai Shi Kotu Kan Sarauta
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya magantu kan rigimar sarautar Kano inda ya fadi babban abin zai saka shi zuwa kotu kan sarauta
- Sanusi II ya ce idan aka tsige shi da zargin badakala ko wani abu na bata suna zai ziyarci kotu domin wanke kansa daga zargi
- Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da shari'a kan rigimar sarautar Kano tsakaninsa da Aminu Ado Bayero
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan rigimar sarautar jihar bayan Aminu Ado Bayero ya shigar da kara kotu.
Sanusi II ya ce ko da an tsige shi a sarauta babu abin da zai sa ya je kotu sai dai idan an cire shi kan zargin da zai bata masa suna.
Sanusi ya yi magana kan sarautar Kano
Mai Martaban ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar The Sun a yau Asabar 15 ga watan Yuni a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce idan har aka cire shi da zargin badakala zai je kotu ne domin wanke kansa saboda mutuncinsa yafi masa komai.
Musabbabin da zai kai Sanusi II kotu
"Na yi sarauta na tsawon shekaru shida, alhamdulillah, na yi abin da zan iya, dalilin da zai sa na je kotu shi ne idan aka cire ni kan zargin da zai batamin suna."
"Dalili kuwa shi ne babban abin da nake mutuntawa fiye da komai shi ne mutunci na."
"Idan har suka zarge ni da badalaka ko wani abu daban, da zan je kotu saboda wanke kai na, amma sun ce wai rashin biyayya ne."
- Muhammadu Sanusu II
Sanusi II ya caccaki Ganduje kan masarautu
A wani labarin, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya soki Abdullahi Ganduje da neman lalata al'adun jihar Kano.
Sanusi II ya ce an shafe fiye da shekaru 1,000 da masarautun Kano amma babu wanda ya bukaci karin wasu.
Sarkin ya ce Abba Kabir ya gyara duka barnar da Ganduje ya tafka lokacin da yake rike da ragamar gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng