Sanusi II Ya Tabo Batun Wani Gwamna Ya Tsige Shi a Gaba, Ya Fadi Matakin Dauka

Sanusi II Ya Tabo Batun Wani Gwamna Ya Tsige Shi a Gaba, Ya Fadi Matakin Dauka

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ba zai damu ba idan wani gwamna ya sake raba shi da sarautar Kano a nan gaba
  • Mai martaba Sarkin ya nuna farin cikinsa kan yadda gwamnatin jihar ta dawo da masarautar Kano yadda aka santa a da
  • Sarkin na Kano ya kuma nuna farin cikinsa cewa ba a lokacinsa ba ne tarihin masarautar na fiye da shekara 1000 zai lalace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan yiwuwar wani gwamna ya tsige shi a nan gaba.

Sarkin na Kano ya bayyana cewa sam ko kaɗan bai damu da hakan ba.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka

Sanusi II ya yi magana kan yiwuwar sake rasa sarautar Kano
Sanusi II ya ce ba zai damu ba idan wani gwamna ya sake tsige daga sarautar Kano Hoto: @masarautarKano
Asali: Twitter

A shekarar 2020 ne tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Sanusi II daga karagar mulki, biyo bayan rashin jituwar da suka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sanusi II ya ce kan sarautar Kano?

Da yake magana da jaridar The Sun, Sanusi II ya ce Allah ne kaɗai ya san tsawon lokacin da zai ci gaba da zama a kan karagar mulki.

"A gare ni, ko yanzu da nake nan, Allah ne kaɗai ya san tsawon lokacin da zan kasance a nan. Zan iya mutuwa gobe. Wani gwamna na iya zuwa gobe ya ce ya cire ni, ba komai."
"Amma zan yi farin ciki idan bai taɓa masarautar ba. Ina farin ciki da cewa ba zan bar tarihin cewa a lokacina ne aka lalata waɗannan shekaru 1000 na tarihi."
"Domin haka ina godiya ga wannan gwamnati, ina godiya ga wannan majalisa da suka yi gyara, cewa mun mayar da masarautar yadda take, kuma Insha Allahu idan na mutu ko na tafi, wanda ya gada zai gaji abin da muke da shi."

Kara karanta wannan

A karon farko, Sanusi II yayi maganar rikicin sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

- Muhammadu Sanusi II

Basarake ya taya Sanusi II murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir mai ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murna.

Muhammad Ilyasu Bashir ya tura sakon murnan ne ga Sanusi II bayan dawowa kan kujerar sarautar Kano a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng