Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka

Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka

  • Muhammadu Sanusi II ya bayyana irin barnar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi a Kano
  • Sanusu II ya koka kan yadda aka shafe shekaru 1000 da masarautun Kano amma Ganduje ya kawo tsaiko
  • Sarkin ya kara da cewa Abba Kabir gyara ya yi a dukkan barnar da gwamnatin da shude ta yi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan rigimar sauratar Kano da ake ciki.

Sanusi II ya ce mayar da shi karagar sarautar jihar gyara ne kan barnar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi.

Sanusi II ya magantu kan irin barnar da Ganduje ya yi kan masarautu
Sarki Muhammadu Sanusi II ya zargi Ganduje da neman lalata al'adun Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: UGC

Masarautun Kano: Sanusi II ya soki Ganduje

Sarkin ya bayyana haka ne yayin wata hira na musamman da jaridar The Sun a Kano.

Kara karanta wannan

A karon farko, Sanusi II yayi maganar rikicin sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Kano ta shafe fiye da shekaru 1000 kuma babu wanda ya bukaci karin masarautu tsawon wannan lokaci.

"Mutanen Kano daya ne, basu bukaci karin masarautu ba, muna fama da matsala ce wanda wani ya rarraba mu."
"Ba kundin tsarin mulkin Najeriya ba ne ya samar da masarautun Kano, suna nan tun kafin Najeriya, tun kafin jihadin Danfodiyo."
"Sun rike wannan sarauta na tsawon shekaru huɗu, sabon gwamna ya zo ya ce dole zai dauki mataki kan farmaki kan al'adunmu."

- Muhammadu Sanusi II

Wannan na zuwa bayan dawowa da Sanusi II kan sarautar Kano da Abba Kabir ya yi bayan rushe masarautun da Ganduje ya kirkiro a 2019.

Dawo da Sanusi II ya bar baya da kura da kura yayin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ci gaba da kasancewa a fadar Nasarawa tare da karbar gaisuwa.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Kotu ta shirya raba gardama, za ta sanar da sahihin Sarkin Kano

Kotu ta ci tarar Abba Kabir N10m

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta ci tarar gwamnatin jihar N10m kan rigimar sarauta.

Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan gwamnatin jihar ta ba da umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Daga bisani, kotun ta yi fatali da bukatar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan tuge Sanusi II daga karagar sarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.