Gwamnati Ta Kirkiro Shirin Musamman ga Matasa Masu Hidimar NYSC

Gwamnati Ta Kirkiro Shirin Musamman ga Matasa Masu Hidimar NYSC

  • Gwamnatin Najeriya za ta ba matasa masu hidimar kasa (NYSC) horo na musamman domin inganta rayuwarsu da farfaɗo da tattali
  • Hukumar NITDA ce ta sanar da haka tare da bayyana cewa za ta yi hadaka da hukumar NYSC wajen ganin samun nasarar shirin
  • Babban Daraktan hukumar NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana irin gudummawar da za su bayar domin tabbatar da shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar NITDA ta bayyana aniyar horar da miliyoyin matsa a Najeriya kan kimiyyar zamani ciki har da masu yiwa ƙasa hidima.

Shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa ya bayyana haka ne a hedikwatar hukumar NYSC da ke babban birnin tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su tafi maƙwabciyarta domin wanzar da zaman lafiya, an jero dalilai

Hidimar NYSC
NITDA za ta horar da masu hidimar NYSC. Hoto: National Youth Service Corps - NYSC
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa za a yi haɗaka ne tsakanin hukumomin NITDA, NYSC da kuma ma'aikatar wasanni da matasa ta kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin matasan da za a horar

Shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa ya ce za a koyar da matasa kimanin miliyan 30 daga sassa daban-daban na Najeriya ciki har da 'yan NYSC.

Kashifu Inuwa ya kara da cewa shirin an samar da shi ne domin cike gurbin da ke da shi a Najeriya na rashin fahimtar tattalin arzikin yanar gizo zuwa shekarar 2027.

Wani ilmi za a koyar da matasan?

Kashifu Inuwa ya bayyana cewa a wannan karon za a mayar da hankali ne wajen ba da horo domin samun cikakkiyar kwarewa.

Kuma za koyar da matasan ne kan kirkirar manhajoji, nazarin bayanai ta yanar gizo, tsaron yanar gizo da harkar kasuwanci a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Bankin duniya: Bayan runtumo bashin $2.25bn, Tinubu ya kuma neman rancen $500m

Martanin daraktan NYSC

Babban daraktan NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya nuna gamsuwa da shirin tare da karɓarsa hannu biyu biyu, rahoton the Nation

Birgediya Janar YD Ahmed ya ce hukumar NYSC za ta yi dukkan kokari wajen ganin shirin bai samu tangarɗa ba.

Za a tallafi matasa masu NYSC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce tana shirin tallafawa masu hidimar kasa domin taimaka musu wajen dogaro da kai da samarwa wasu matasan ayyukan yi.

Ministar matasa, Dr. Jamila Ibrahim da ta bayyana hakan ta ce za a rabawa matasan da ke hidimaar kasa 5000 kudi N10m domin bunkasa sana’arsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng