Cin Amana Ya Jawo NDPC Ta ci Bankuna 4 da Wasu Kamfanoni Tarar N400m

Cin Amana Ya Jawo NDPC Ta ci Bankuna 4 da Wasu Kamfanoni Tarar N400m

  • Hukumar kare bayanan ‘yan Najeriya ta bayyana cewa sun ci tarar manyan kamfanoni ciki har da bankuna guda hudu N400m ssaboda samunsu da laifin shiga bayanai
  • Shugaban hukumar, Vincent Olatunji ne ya bayyana haka inda ya ce wannan ya biyo bayan amfani da bayanan ‘yan kasa da su ka yi ba bisa ka’ida ba wanda ya saba doka
  • Ya ce sun bincike manyan bankuna da kamfanonin da ke bayar da bashi ta kafar yanar gizo, makarantu da kamfanonin inshora akalla 1000 bisa zargin kutsawa cikin bayanan jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar kare bayanan ‘yan kasa (NDPC) ta ce ta na binciken akalla kamfanoni, bankuna, makarantu, kamfanonin inshora, cibiyoyin kasuwanci 1000 da ake zargi da amfani da bayanan al’umma ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

Shugaban hukumar, Vincent Olatunji da ya bayyana haka ya ce sun ci manyan bankuna hudu a kasar nan da wasu cibiyoyi tarar N400m da ma wasu hukunce hukunce saboda kutsawa cikin bayanan abokan huldarsu.

Bayanai
Hukumar NDPC ta binciki kamfanoni 1000 bisa zargin kutsawa bayanan jama'a Hoto: MTStock Studio
Asali: Getty Images

Punch News ta wallafa cewa Olatunji ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai kan bikin cika shekara daya da sa hannu kan dokar da ta kafa hukumarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Za mu kare bayanan ‘yan kasa,’ NDPC

Shugaban hukumar kare bayanan ‘yan Najeriya, Vincent Olatunji, ya ce tun bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa bangaren bayanan ya girma da N10bn.

Ya ce sun yi tsayin daka wajen tabbatar da kare dukkanin bayanan yan kasa domin kare rayuwarsu kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Vincent Olatunji, ya kara da cewa cikin korafe-korafe kimanin 1000 kuma, 400 daga cikin kamfanonin da aka bincika na aiki bayar da rance ta kafar intanet.

Kara karanta wannan

Hajj: Najeriya ta kammala jigilar alhazanta zuwa kasa mai tsarki

Ya bayyana cewa wadanda ake bincike a halin yanzu su ne na bangaren ilimi, hada-hadar gidaje da filaye, kamfanonin da ke mu’amalantar kudi da kamfanonin inshora.

EFCC ta kwato kadadrori da aka sace

A baya mun kawo maku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta samu nasarar kwato wasu kadarori da kudin da wasu ‘yan gida daya suka sace.

Wata babbar kotu a Abuja ta sahalewa hukumar EFCC kwace kadarorin da Olisaebuka Eze da Onyeka Eze suka sacewa Arthur Eze a shekarar 2022, ciki har da motoci da agogon hannu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.