12 ga Yuni: 'Yar'Adua, Abiola da Mutane 30 da Suka Tabbatar da Dimokuradiyyar Najeriya
Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya lissafa sunayen wasu 'yan mazan jiya da ya ce su ne suka sadaukar da rayuwarsu domin tabbatar dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Shugaba Bola Tinubu ya ce shekaru 31 da suka gabata, Najeriya ta tsaya tsayin daka domin ganin cewa ta koma kan turbar mulki na dimokuraɗiyya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin kai tsaye da ya gabatar a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, kamar yadda hadimin Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
A jawabin zagayowar ranar dimokuraɗiyyar Najeriya na shekarar 2024, Tinubu ya lissafa wadanda suka tabbatar da dimokuraɗiyyar ƙasar na shekaru 25.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya lissafo gwarazan dimokuraɗiyya
Ga jerin akalla mutane 32 da Shugaba Tinubu ya ayyana a matsayin gwarazan dimokuraɗiyyar Najeriya.
- Cif MKO Abiola
- Kudirat Abiola
- Janar Shehu Musa Yar’Adua
- Pa Alfred Rewane
- Chif Anthony Enahoro
- Chif Abraham Adesanya
- Commodore Dan Suleiman
- Chif Arthur Nwankwo
- Chif Chukwuemeka Ezeife
- Admiral Ndubuisi Kanu
- Chif Frank Kokori
- Chif Bola Ige
- Chif Adekunle Ajasin
- Chif Ganiyu Dawodu
- Chif Ayo Fasanmi
- Chief Gani Fawehinmi
- Chief Olabiyi Durojaiye
- Dakta Beko Ransome-Kuti
- Chima Ubani
- Janar Alani Akinrinade
- Farfesa Bolaji Akinyemi
- Farfesa Wole Soyinka
- Chif Ralph Obioha
- Chif Cornelius Adebayo
- Olisa Agbakoba
- Femi Falana
- Abdul Oroh
- Sanata Shehu Sani
- Gwamna Uba Sani
- Chif Olu Falae
- Chif Ayo Adebanjo
- Chif Ayo Opadokun
Karanta jawabin Tinubu a nan kasa:
An gano kura-kurai a taken Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ba hukumar wayar da kan jama'a ta kasa (NOA) umarnin yin gyara a sabon taken Najeriya.
Shugaban majalisar dattawa ya gano wasu kura-kurai a ɗangwaye na uku, biyar da 18 na sabon taken ƙasar wanda hukumar NOA ta gabatar a makon jiya.
Haka zalika, Sanata Godswill Akpabio ya zargi hukumar da gabatar da kasafin da ba shi ne majalisar tarayya ta amince da shi ba yana mai kira ga NOA da ta gaggauta gyara kurakuran.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng