Gobara Ta Tashi a Kwalejin Fasaha a Jihar Kano, Wuta Ta Jawo an Tafka Asara Mai Yawa
- Wata mummunar gobara ta tashi a kwalejin fasaha ta jihar Kano da safiyar yau Talata, inda ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa
- An ruwaito cewa gobarar ta babbake kafatanin sashen koyon Arts and Industrial na kwalejin da ke a bangaren koyon fasaha na kwalejin
- Kakakin hukumar kashe gobara na Kano, Saminu Abdullahi wanda ya tabbatar da lamarin ya ce har yanzu ba a gano musabbabin wutar ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - An tashi cikin wani mummunan yanayi a jihar Kano bayan da wata gobara ta babbake ilahirin bangaren koyon ilimin fasaha da ke a cikin kwalejin fasaha ta Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta babbake kafatanin sashen koyon ilmin fasaha da na masan'antu na kwalejin a safiyar yau Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobara ta babbake kwalejin Kano
Saminu Abdullahi wanda ya ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar, ba ya ce wutar ta lakume dukiya mai yawa amma ba a kammala tantance wa ba.
A cewarsa hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani Faisal Dauda wanda ya ba da rahoton cewa an samu tashin gobara a kwalejin fasahar.
Mista Saminu ya bayyana cewa ginin mai dauke da ajujuwa tara da ofisoshi shida ya lalace gaba daya.
Kakakin hukumar kashe gobarar ya yi nuni da cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma ana ci gaba da binciken musabbabin wutar.
Gwamnatin Kano za ta biya Doguwa N25m
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotu da ke jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya Alhassan Ado Doguwa diyyar Naira miliyan 25.
A cikin takardar hukuncin da kotun ta yanke mai lamba FHC/ABJ/ABJ/CS/714/2019, an wanke Hon. Ado Doguwa daga zargin kisan kai.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin NNPP a Kano ta gurfanar da Doguwa a gaban kotu ne kan zargin mutuwar mutane akalla 15 a zaben zaben shugaban kasa na 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng