Bankin CBN Ya Soke Lasisin Wasu Manyan Bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya Ta Fito

Bankin CBN Ya Soke Lasisin Wasu Manyan Bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya Ta Fito

  • Bankin CBN ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris, Wema da kuma Unity
  • Muƙaddashiyar kakakin CBN, Hakama Sidi Ali, ta yi ƙarin haske kan takardar da ke yawo a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni
  • Ta bukaci abokan hulda su kwantar da hankalinsu domin kuɗafen da suka ajiye a asusunsu na nan cikin aminci da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata zargin da ake masa na cewa yana shirin soke lasisin aiki na bankunan Fidelity, Polaris, Wema, da Unity.

Babban bankin ya yi wannan bayanin ne yayin da mutane suka fara shiga damuwa kan makomar bankunan ƙasar nan biyo bayan soke lasisin Heritage.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso.
Bankin CBN ya musanta soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris. Wema da Unity Hoto: @cenbank
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Hakama Sidi Ali, mukaddashiyar daraktan sashen sadarwa ta bankin CBN ta fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tabbatarwa kwastomomi cewa duk kuɗin da suka ajiye a banki na nan cikin aminci kuma babu abin da zai taɓa su, The Nation ta tattaro.

CBN ya faɗi gaskiya kan soke lasisi

Hakama Sidi ta kuma yi ƙarin haske kan wata sanarwa da CBN ya fitar tun a ranar 10 ga watan Janairu, 2024 wadda ta rushe majalisar gudanarwa a bankunan Keystone da Polaris.

Legit Hausa ta fahimci cewa a yanzu ana ta yaɗa wannan sanarwa da ikirarin CBN ya fitar da ita ne yau Litinin, 10 ga watan Yuni, wanda ko kaɗan ba haka bane.

Kakakin CBN ya bayyana cewa wannan sanarwa ba ta yanzu ba ce, tsohon mataki ne da babban bankin ya ɗauka watannin da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shari'ar sarautar Kano, Abba ya biya wa ɗalibai 119,903 kudin NECO

Lasisin bankin Heritage da CBN

"Lamarin bankin Heritage na daban ne," in ji Hakama, inda ta ƙara da cewa rahoton da ke yawo cewa ana shirin sake soke lasisin wasu bankuna ba gaskiya ba ne.

Hakama ta kuma yi kira ga kwastomomi musamman waɗanda suka ajiye kuɗaɗensu a bankin Heritage kada su damu ko fargabar rasa haƙƙoƙinsu, cewar Leadership.

Kotu ta kwace kadarorin Emefiele

A wani rahoton kuma, Kotu ta bayar da umarnin a kwace wasu manyan kadarorin maƙudan kuɗi na tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya mai zama a Legas ne ya bayar da wannan umarnin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262