'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarna, Sun Tafi da Matafiya da Yawa a Hanyar Zuwa Abuja

'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarna, Sun Tafi da Matafiya da Yawa a Hanyar Zuwa Abuja

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama yayin da suke hanyar zuwa birnin tarayya Abuja daga jihar Enugu
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Nasarawa-Keffi
  • Ya ce tuni jami'an tsaro suka fara aiki ba dare ba rana domin ceto dukkan fasinjojin da kuma kamo ƴan bindigar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjojin da suka taso daga jihar Enugu da nufin zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan sun yi garkuwa da matafiyan ne yayin da suka farmaki wata motar Bas mai cin mutum 18 a jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ɗauki zafi, an dakatar da wasu manyan jiga jigan jam'iyya

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Fasinjojin da suka taso daga Enugu zuwa Abuja sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane a Nasarawa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ne ya tabbattar da haka ga Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace fasinjojin Abuja

Nansel wanda ya bayyana hakan a daren Juma’a, ya ce ‘yan sanda sun samu labarin cewa an kai farmaki kan wata motar bas mai fasinjoji 18 da ta taso daga Enugu zuwa Abuja

Kakakin ƴan snadan ya ce maharan sun tare motar ne a daidai kauyen Doruwa da ke kan titin Nasarawa zuwa Keffi, sannan sun tafi da fasinjoji da yawa.

Ya kara da cewa daga baya ƴan sanda da wasu jami'an tsaro sun kubutar da uku daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da suka kai ɗauki yankin.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

“Jami’an ‘yan sanda tare da hadin guiwar wasu jami’an tsaro sun kai ɗauki cikin gaggawa, sai dai rahoton faruwar lamarin ya isa ga jami'an tsaro bayan maharan sun gama aikata nufinsu."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja, an kama miyagu

"Mun bi diddikin maharan tare da baza jami'an tsaro a yankin, wanda daga bisani aka ceto mutum uku, yanzu haka an kai motar ofishin ƴan sanda."

- DSP Ramhan Nansel.

Nansel ya ce jami'an tsaro na ci gaba da aiki ba kama hannun yaro da nufin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma cafke maharan, rahoton Vanguard.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

A wani rahoton kuma miyagun ƴan bindiga sun kai kazaman hare-hare kan bayin Allah a ƙananan hukumomin Safana da Dutsinma a jihar Katsina.

Ganau sun bayyana cewa ana fargabar maharan sun kashe akalla mutane 30 yayin da wasu da dama suka tsere suka bar gidajensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262