Sojoji sun Kara Samun Nasara, an Harbe 'yan Ta'adda a Kaduna

Sojoji sun Kara Samun Nasara, an Harbe 'yan Ta'adda a Kaduna

  • Rundunar sojojin kasar nan ta samu galaba a kan wasu 'yan ta'adda da suka addabi jama'ar Kaduna a wani sharar bata-gari a yankunan jihar da dama
  • Kwamishinan harkokin tsaron ciki gida a jihar, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jami'an sun kashe 'yan ta'adda biyu a karamar hukumar Kachia
  • Yankunan da jami'an su ka gudanar da ayyukansu sun hada da Amale, Gidan Jatau, da Gidan Dutse, inda da yawa daga cikin miyagun su ka tsere da raunukan bindiga

Jihar Kaduna- Yayin da rashin tsaro ke ci gaba da barazana ga zaman kwanciyar hankali a sassan Arewacin Najeriya, rundunar sojojin kasar nan ta sake samun nasara kan ‘yan ta’adda a jihar Kaduna.

Dakarun operation Whirl Punch da Operation Forest Sanity II sun samu nasarar kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan yankin Rijana a karamar hukumar Kachia.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan tsige ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC

Sojoji
Sojoji sun farmaki yan ta'adda a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na facebook, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro a Kaduna, Samuel Aruwan ya ce dakarun sun fatattaki ‘yan ta’adda a yankuna da dama a jihar.

Dakaru sun yi sharar ‘yan ta’adda

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa dakarun sojojin kasar nan sun yi sharar ‘yan ta’adda a yankunan Amale, Gidan Jatau, Gidan Danfulani da Gidan Duna ba tare da samun tirjiya ba, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce dakarun sun isa yankin Gidan Dutse, a nan ne su ka yi artabu da ‘yan ta’adda har aka kashe biyu daga cikinsu.

Samuel Aruwan ya kara da cewa an samu kwato bindigogi kirar AK-47, babura guda biyu, alburusai da wayoyin hannu, yayin da wasu daga ‘yan ta’addar su ka tsere da raunuka.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja, an kama miyagu

Rundunar sojoji ta karyata kisan kabilar Ibo

A wani labarin kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta magantu kan zargin da 'yan ta'adda na cewa jami'anta sun kashe wasu 'yan kabilar Ibo.

Rundunar ta ce zargi ne kawai mara tushe ballantana makama da kokarin tayar da fitina a zukatan jama'a, inda ta ce mutanen da ake zargi da kisan ba jami'anta ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel