Mafi Karancin Albashi: Shehu Sani Ya Yiwa N62,000 da Gwamnati Tayi Ga Ma’aikata Fashin Baki
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana gaskiyar ma'anar sabon tsarin mafi karancin albashin ma'aikata na N62,000
- Shehu Sani ya ce N60,000 na nuna shiyyoyi shida na siyasa a Najeriya, yayin da N2000 ke wakiltar babbar birnin tarayya (FCT)
- 'Yan Najeriya sun maida martani kan batun Shehu Sani, suna bayyana karin N2000 akan N60,000 din a matsayin abin kunya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan sabon tsarin gwamnatin tarayya na mafi karancin albashin ma'aikata na N62,000 a kasa baki daya.
Legit ta ruwaito cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta kara tayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N62,000 daga N60,000.
Adadin ya tabbata ne yayin da batun ya fito daga bakin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC masu ci (PGF).
Martanin Shehu Sani kan N62,000
Tsohon dan majalisar tarayyar, Shehu Sani ya ce N62,000 na nufin N10,000 ga kowacce shiyyar siyasa daga shiyyoyi shida na kasar, yayin da N2000 ke wakiltar babbar birnin tarayya (FCT).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X, @ShehuSani a ranar Juma'a, 7 ga watan Yunin wannan shekarar.
Shehu Sani ya rubuta:
"62k na nufin 10k ga kowanne daga cikin shiyyoyi shida na siyasa, 2k kuma na wakiltar FCT."
'Yan Najeriya sun maida martini ga batun Shehu Sani
Legit.ng ta tattaro wasu daga abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa kan sabon tayin mafi karancin albashin ma'aikata na N62,000.
@okparajoyf:
"Kungiyar kwadago sub a da hakuri su dawo bakin aiki kawai. Wata rana su nemi a dawo da farashin man fetur kamar yadda yake a baya. Su dage akan a rage albashi da alawus din 'yan siyasa gaba daya."
@KayMurphy01:
"Dangane da halin da ake ciki, 62k ba komai bane a yanzu, ba dukkan gwamnoni ne za su biya ba. Har yanzu 30k wasu ba su biya ba hmm... Duk da haka Allah ya albarkaci Najeriya."
@Nas120362910:
"Na san za a rina, sun ce za su kara kan N60k da aka fara tattaunawa a kai, kuma NLC ta amince da hakan, yanzu sun kara N2000."
Gwamnoni ne matsalar Najeriya, inji 'yan kasa
A wani labarin, gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya a jiya Juma’a 7 ga watan Yuni sun yi watsi da shawarar gwamnatin tarayya na ba ma’aikata N60,000 matsayin mafi karancin albashi.
Daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Wannan na zuwa ne a yayin da 'yan Najeriya ke jiran kammala tattaunawar gwamnati da kungiyar kwadago kan sabon mafi karancin albashi a kasar.
Asali: Legit.ng