Mafi Karancin Albashi: ’Yan Najeriya Sun Gano Tushen Matsalolin Kasa, Sun Ambaci Suna
- Yayin da gwamnatin Najeriya ke bayyana amincewa da kara albashin ma’aikata, gwamnoni sun zama babbar matsala ga jihohinsu
- ‘Yan Najeriya sun bayyana kuka kan yadda gwamnoni ke korafin ba za su iya biyan mafi karancin albashin N60,000 ba
- An shawarci NLC da ta ki amincewa da albashin, lamrin da ake sa ran zai kawo sauyi ga goben ma’aikata a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Najeriya - Gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya a jiya Juma’a 7 ga watan Yuni sun yi watsi da shawarar gwamnatin tarayya na ba ma’aikata N60,000 matsayin mafi karancin albashi.
Daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Wannan na zuwa ne a yayin da 'yan Najeriya ke jiran kammala tattaunawar gwamnati da kungiyar kwadago kan sabon mafi karancin albashi a kasar.
Gwamnoni ne matsalar Najeriya, inji ‘yan kasa
Sai dai, nuna kin amincewa da gwamnonin suka yi ya ja ‘yan Najeriya tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta bayyana martanin da wani dan Najeriya mazaunin Abuja ya yi, inda ya ce:
“Babu shaka gwamnonin ne babbar matsalar wannan kasar! Suna cewa ba za su iya biyan N60,000 ba amma suna yin rayuwa mai kyau suna wadaka da kudin jama'a kan abubuwa marasa muhimmanci. Wannan abin takaici ne.”
Ba wannan ne kadai mai martani kan lamarin ba, Legit ta tattauna da wani malamin makarantar sakandare ta gwamnatin jiha da ke Gabukka a jihar Gombe, M.A Sani, inda yace:
“Gaskiya gwamnoni ba sa tsoron Allah. Ai sun iya dauko ayyukan da ba za su amfane mu ba, sai su rage don biyan ma’aikata albashi.”
Ta ma’aikata ake, mu leburori an barmu a baya
Wani mazaunin jihar Gombe, Muhammad Rabiu ya bayyana kukansa, inda yace sam ko da an yi karin ba lallai wadanda ba sa aikin gwamnati su amfana ba.
A cewarsa:
“Ma’aikata za su samu kari, mu kuma da muke leburanci sai dai mui ta addu’a. Ga karin haraji ga tsadar rayuwa sannan ba a ma ta mu leburori.”
Tarihin mafi karancin albashi a Najeriya
A tarihin Najeriya, an sha sauya mafi karancin albashi a lokuta mabambanta domin shawo kan lamarin da ya shafi rayuwar ma'aikata.
Rahoton da wakilin Legit Hausa ya tattara ya bayyana yadda a tsawon tarihi aka samu sauyin albashin a karkashin shugabanni da dama.
Kadan daga dalilan sauya albashin akwai tsadar kayayyaki da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar.
Asali: Legit.ng