Yadda Gwamnatin Sokoto Ta Ceto Mutum 250 Daga Hannun 'Yan Bindiga

Yadda Gwamnatin Sokoto Ta Ceto Mutum 250 Daga Hannun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana irin nasarorin da ta samu a ƙoƙarin da take yi na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar
  • A cikin shekara daya gwamnatin ta samu nasarar ceto mutum 250 daga hannun ƴan bindiga waɗanda tuni aka mayar da su zuwa garuruwansu
  • Mai ba gwamnan jihar shawara ta musammman kan harkokin tsaro ya bayyana hakan inda ya ƙara cewa gwamnatin ta kuma samar da kayan aiki ga rundunar tsaron jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ta ceto mutane sama da 250 daga hannun ƴan bindiga.

Hakan na cikin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na daƙile matsalar rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Gwamnatin Sokoto ta ceto mutane daga hannun 'yan bindiga
A cikin shekara daya gwamnatin Sokoto ta ceto mutum 250 daga hannun 'yan bindiga Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Gwamnatin a cikin shekara ɗayan farko ta kuma kafa rundunar tsaro domin maganin rashin tsaro a jihar da taimakawa sauran hukumomin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma'a a shirye-shiryen da ake na cikar gwamnatin shekara ɗaya, cewar rahoton Tribune.

Nasarorin gwamnatin Sokoto a ɓangaren tsaro

Ya bayyana cewa gwamnatin domin tabbatar da ana gudanar da ayyuka yadda ya kamata, ta siyo motoci 40 ƙirar Toyoto Hilux domin sabuwar rundunar tsaron da aka kafa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar ta shirya raba babura 1000 ga jami'an sabuwar rundunar tsaron.

Sauran nasarorin da gwamnatin ta samu a ƙasa da shekara ɗaya sun haɗa da:

"Saye da raba motoci 72 da suka haɗa da Toyota Hilux da Buffalo ga jami’an tsaro domin samar da ingantaccen tsaro a jihar."

Kara karanta wannan

NLC: Minista ya yi magana kan sabon mafi ƙarancin albashi bayan ya gana da Bola Tinubu

"Biyan kuɗaɗen tallafi ga hukumomin tsaro wanda ya kai ga ceto sama da mutane 250 daga hannun ƴan bindiga waɗanda tuni suka koma garuruwansu lami lafiya."

Gwamnati na ƙoƙari kan tsaro

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Sokoto mai suna Muhammad Bashir, wanda ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen samar da tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a shekara ɗaya da gwamnatin ta yi akan mulki a ɓangaren samar da tsaro.

"Eh tabbas wannan rundunar da aka samar suna ƙokari sosai wajen samar da tsaro kuma al'amura sun fara daidaita a yanzu."

- Muhammad Bashir

Gwamnatin Sokoto ta rufe otel

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rufe otel ɗin Ifoma da ke cikin jihar bisa zargin aikata ayyukan ɓarna.

Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto ne ya bayar da umurnin kulle hotel din biyo bayan korafi da al'ummar garin suka shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel