Alhazan Kano Sun Samu Gata, An Fara Ciyar da Su Abinci Kyauta a Saudiyya

Alhazan Kano Sun Samu Gata, An Fara Ciyar da Su Abinci Kyauta a Saudiyya

  • Gwamnatin jihar Kano ta fara ciyar da alhazan jihar sau biyu a kowace rana a masaukinsu da ke ƙasar Saudiyya
  • A wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamna, Shu'aibu Ibrahim, ya fitar ya ce gwamnati ta tura kwararrun likitoci su kula da maniyyatan Kano
  • Har ila yau gwamnatin ta tura tawagar kula da mahalli waɗanda za su tabbatar da aminci da tsaftar masaukin alhazan Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Gwamnatin Kano ta ce tana baiwa alhazan jihar da a halin yanzu suke kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana na 2024 abinci kyauta sau biyu a kullum.

Mai magana yawun alhazan jihar Kano kuma kakakin mataimakin gwamnan jihar, Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi albishir yayin da ta bayyana ƙoƙarinta wajen shawo matsalolin Najeriya

Alhazai a Masallacin harami.
Gwamnatin Kano tana ciyar da alhazai sau biyu a kowace rana a Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Ya ce gwamnati ta fara ciyar da alhazan ne domin tabbatar da walwala da jin dadinsu a tsawon lokacin da za su shafe a ƙasa mai tsarki, jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya kara da cewa ana bayar da abincin sau biyu a rana ga daukacin alhazan jihar Kano, ba tare da la’akari da matsayinsu ko dukiyarsu ba.

"Abincin, wanda tawagar ƙwararrun masu dafa abinci ke girkawa, sun haɗa da masu gina jiki da daɗi, kuma ana yin su ne a cikin tsafta da muhalli mai tsafta,” in ji shi.

Gwamnatin Kano ta tura likitoci

Baya ga abincin, gwamnatin jihar Kano ta kuma tura tawagar kwararrun likitocin kasar Saudiyya domin kula da lafiyar alhazai.

Tawagar likitocin da ta hada da likitoci, ma’aikatan jinya, da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya, tana sansanin alhazai na jihar Kano da ke Makkah.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta kuma tura tawagar kula da muhalli domin tabbatar da aminci da tsaftar muhallin mahajjata.

"Alhazai da masu ruwa da tsaki sun yaba, inda suka yabawa gwamnati bisa jajircewar da ta yi wajen kyautata rayuwar al’ummarta a kasa mai tsarki,” in ji sanarwar.

Ƴar Najeriya ta rasu a Madinah

A wani rahoton kuma Allah ya yiwa wata Hajiya wacce ta fito daga jihar Neja rasuwa a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Hajiyar mai suna Ramatu Abubakar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madina bayan ta kamu da rashin lafiya daga isarsu ƙasa mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel