Sarauta: Yadda Lauyoyi Suka Gwabza a Shari'ar Aminu Ado Bayero da Gwamnatin Kano
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tanadi hukunci kan karar da mai martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya shigar kan batun haƙƙinsa.
Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda, ya tanadi hukuncin biyo bayan zazzafar muhawara tsakanin lauyoyin kowane ɓangare.
Aminu Ado Bayero ya kai kara kotu
Daily Trust ta ruwaito cewa Aminu Ado ya shigar da kara gaban kotun ne domin neman ta hana gwamnatin Kano da sauransu kama shi ko tauye masa haƙƙi.
Waɗanda basaraken yake kara a shari'ar sun haɗa ba Antoni Janar na ƙasa, gwamnatin Kano/Antoni-Janar na jihar, rundunar ƴan sanda, IGP, da kwamishinan ƴan sanda na Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran su ne hukumar DSS, rundunar NSCDC, sojojin ƙasa, sojojin sama da sojojin ruwa. Sarki Aminu Ado ya nemi kotu ta hana su kama shi ko tauye masa haƙƙi.
Kano: Yadda lauyoyi suka yi zazzafar muhawara
Yayin da aka dawo zaman shari'ar ranar Jumu'a, lauyan gwamnatin Kano Mahmoud Abubakar Magaji, ya roƙi kotu ta yi watsi da ƙarar Sarki Aminu Ado.
Lauyan ya shaidawa kotu cewa:
"Zama sarki alfarma ne ba haƙƙi ba kuma wanda ya kawo ƙarar (Aminu Ado Bayero) ya shigar da ita ne kwanaki biyar bayan an tsige shi. Ba shi ne sarkin Kano ba a lokacin da ya kawo ƙara."
"Mai kara ya amince an sauke shi daga sarauta don haka ina rokon mai shari'a ya duba kar ya saurari wannan buƙata."
Bayan haka Magaji ya shigar da buƙatar kotu ta soke umarnin da ta bayar a baya na hana kama sarki na 15, Aminu Ado Bayero, jaridar Vanguard ta ruwaito wannan.
Lauyan Aminu Ado ya mayar da martani
A nasa ɓangaren lauyan Sarki Aminu, Michael Jonathan Numa ya ce kotu na da hurumin sauraren wannan batu domin ya shafi hakkokin mai ƙara.
Ya kuma yi jayayya da lauyan gwamnati, yana mai roƙon kotu ta amince da wannan buƙata domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a Kano.
A farkon zaman lauyan ya sanar da Kotun cewa sun janye buƙata ta ɗaya da ta biyu daga cikin buƙatun da suka gabatar.
Bayan kammala sauraren kowane ɓangare, alkalin kotun ya ɗage zaman, ya ce za a sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.
Gwamnoni sun yi watsi da biyan N60,000
A wani rahoton kuma ƙungiyar gwamnoni 36 a Najeriya (NGF) ta ce mambobinta ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ba.
Mai magana da yawun NGF, Hajiya Halima Salihu ta ce kuɗin sun yi yawa kuma gwamnoni ba za su iya jure biya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng