Kamfanin Rarraba Wuta Zai Yanke Lantarki a Gidajen Gwamnati 5, CBN, NDLEA da Jami'o'i

Kamfanin Rarraba Wuta Zai Yanke Lantarki a Gidajen Gwamnati 5, CBN, NDLEA da Jami'o'i

  • Kamfanin raba wutar lantarki a shiyyar Kudu maso gabas (EEDC) ya yi barazanar katse wuta a manyan ma'aikatun yankin
  • Cikin ma'aikatun da kamfanin zai yankewa wuta akwai gidajen gwamnatin yankin guda biyar, jami'o'i da manyan kamfanoni
  • Har ila yau kamfanin ya bayyana dalilan da suka sa ya dauki matakin katse wutar da kuma wa'adin da zai zartar da hukuncin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Kamfanin rarraba wutar lantarki a kudu maso gabas (EEDC) ya yi barazanar yanke wuta ga manyan ma'aikatun gwamnati da kamfanoni a yankin.

Cikin wuraren da barazanar ta shafa akwai gidajen gwamnatocin yankin, jami'ar Nnamdi Azikiwe, barikin sojoji da sauran manyan ma'aikatu.

Kara karanta wannan

"Dalili 1 da ya sa NLC ke zuzuta albashin ƴan majalisun tarayya", inji Hon. Rotimi

EEDC ENUGU
Kamfani zai yanke wuta ga gidajen gwamnati saboda bashi. Hoto: Enugu Electricity Distribution PLC - EEDC
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kamfanin EEDC ya dauki matakin yanke wutar ne saboda tarin bashi da ya biyo su kuma suka gagara biya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe EEDC zai katse wuta?

A cikin sanarwar da kamfani ya fitar a yau Jumu'a, 7 da watan Yuni ya gargadi dukkan waɗanda yake bi bashi da gaggawar biya.

Ya ce duk wadanda suka gaza biyan bashin da yake binsu daga yau zuwa ranar Litinin, 10 ga watan Yuni zai yanke musu wuta ba sani ba sabo.

Meyasa EEDC zai datse wutar lantarki?

Kamfanin EEDC ya ce ya dauki matakin ne saboda tarin bashi da yake bi wanda yake barazana ga harkokinsa, rahoton Premium Times.

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce idan bai dauki matakin ba, da wahala ya iya cigaba da rarraba wutar lantarki ga sauran al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Ma'aikatun da suka ci bashin wuta

Daga cikin manyan ma'aikatun da EEDC ke bi bashi akwai:

  1. Gidajen gwamnatocin yankin biyar
  2. Kamfanin kere-keren Innoson
  3. Jami'ar Nnamdi Azikiwe
  4. Barikin sojoji
  5. Ofisoshin yan sanda
  6. Ofisoshin babban bankin Najeriya (CBN)
  7. Ofishin NDLEA
  8. Jami'ar jihar Ebonyi
  9. Asibitin koyarwa da ke Abakaliki
  10. Sakateriyar gwamnatin tarayya, da dai sauransu.

NLC ta katse lantarki a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa a lokacin da take yajin aiki.

An ruwaito cewa an rufe ginin tushen wutar da misalin karfe 2:19 na safiyar ranar Litinin da ta wuce, abin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng