Gwamnati Ta Yi Albishir Yayin da Ta Bayyana Ƙoƙarinta Wajen Shawo Matsalolin Najeriya

Gwamnati Ta Yi Albishir Yayin da Ta Bayyana Ƙoƙarinta Wajen Shawo Matsalolin Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ba yan Najeriya hakuri tare da kiransu da su kara juriya kan matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya bayyana haka a yayin wani taro da kungiyar CAN ta shirya a Najeriya
  • Sanata George Akume ya bayyana matakin da gwamnatin da dauka domin ganin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Gwamantin tarayya ta yi kira ga daukacin yan Najeriya kan kwantar da hankali dangane halin da ake ciki na tsananin rayuwa.

Sakataren gwamnatin, Sanata George Akume ne ya bayyana haka tare da cewa sun dauki matakin kawo saukin rayuwa a kasar.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bukaci ayi gaggawan fito da shi, sun gabatar da hujjoji

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya ta ce sauki na zuwa nan gaba kadan. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata George Akume ya fadi haka ne yayin taron majalisar zartarwar kungiyar CAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da gwamnati ta dauka kan matsi

Sanata George Akume ta bayyana cewa daga cikin matakin da suka dauka na kawo saukin rayuwa akwai kashe N100b domin samar da motocin zirga zirga.

George Akume ya kara da cewa sun ware N125b domin kara karfafan masu kananan sana'o'i a fadin Najeriya.

Har ila yau ya ce gwamnati ta ware N200b domin tallafawa bangaren noma a Najeriya, rahoton Pulse Nigeria.

Ya tabbatar da cewa wannan duk suna cikin kokarin da gwamnatin ta yi domin ganin an samu sauƙin rayuwa bayan cire tallafin man fetur kuma akwai tabbas cewa saukin zai zo.

Akume ya yi kira ga yan kwadago

A yayin taron, George Akume ya yi kira ga yan kwadago kan kada suyi gaggawar yanke hukunci alhali ana tattaunawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Ya kuma bayyana cewa katse wutar lantarki da suka yi a lokacin yajin aiki abu ne da ba shi da wata fa'ida domin babu inda ake haka a duniya.

Gwamnatin Tinubu ta gaza cika alkawura

A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana manyan alkawuran da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gaza cikawa bayan ya shafe shekara guda a kan mulki.

Daga cikin alkawuran da Bola Tinubu ya yi akwai farfaɗo da darajar Naira da kuma inganta rayuwar al'ummar Najeriya amma cikin shekara daya hakan ya gagara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel