Ruwa Yayi Gyara: Mamakon Ruwa da Iska Ya Lalata Gidaje 100, An Rasa Muhalli a Plateau
- Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya raba mutane sama da 100 a jihar Plateau da gidajensu bayan an kusan kwana ana ruwan a ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da ta Kudu
- Ruwan wanda ya fara da tsakar dare ya cire saman kwanon wasu gidajen, inda wasu koma ya cire musu kofofi kuma ya bar mutanen cikin halin n thei 'ya su na rashin muhalli
- Unguwannin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Jenta Adamu, Kabong, Angwan Rogo da Zololo wanda wasu daga mutanen da iftila'in ya rutsa da su ke cikin wani hali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Plateau- Mamakon ruwan dare da ya sauka a jihar Plateau ya janyo ɗimbin asara ga mazauna ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da ta kudu. Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara kamar da misalin ƙarfe 1:00 na dare ya raba mutane sama da 100 da matsugunsu.
Daily Trust ta tattaro cewa ruwan ya lalata gidaje fiye da 100 ta hanyar cire musu rufin kwano, kuma wuraren da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Jenta Adamu, Kabong, Angwan Rogo da Zololo.
Wane hali mutane ke ciki bayan ruwan?
Mazauna yankunan da iftila'in mamakon ruwa mai ta'adi ya rutsa da su sun bayyana fargaba kan halin da suka tsinci kansu a ciki da safiyar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani magidanji da lamarin ya rutsa da shi, Ibrahim Musa mazaunin titin Bauchi ya ce iskar da ta biyo ruwan ta cire masa kofar gidansa.
Emmanuel Shang, shi ma guda ne daga waɗanda iftila'in ya rutsa da shi, ya shaida cewa yanzu haka shi da iyalansa sun zama abin tausayi saboda sun rasa gidansu.
Mamakon ruwa: An rasa rai a Bauchi
A wani labarin kun ji yadda mutane biyar suka kwanta dama a jihar Bauchi bayan wani mamakon ruwa kamar da bakin kwarya a daren Asabar.
Ruwan ya fara ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda rumfunan kasuwar da ake bikin baje kolin kasuwanci na haɗin gwiwa na shiyyar Arewa maso gabas karo na 15 a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng