Lauyoyin Nnamdi Kanu Sun Bukaci Ayi Gaggawan Fito da Shi, Sun Gabatar da Hujjoji

Lauyoyin Nnamdi Kanu Sun Bukaci Ayi Gaggawan Fito da Shi, Sun Gabatar da Hujjoji

  • Gwamnatin Najeriya ta cigaba da rike jagoran yan a-ware masu fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu tun shekarar 2021
  • Ana zargin Nnamdi Kanu ne da laifuffuka da dama wada suka hada da cin amanar kasa da hannu cikin ayyukan ta'addanci
  • Bayan shafe shekaru ana zuwa kotu, lauyoyin Kanu sun tura hujjoji da dama suna bukatar gwamnati ta sake shi da gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Bayan shafe shekaru ana shari'a kan zargin Nnamdi Kanu, lauyoyinsa sun tura takarda ga gwamnati kan a sake shi.

Nnamdi Kanu ya kasance shugaban yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Kotu ta yi umarnin buga sammacin shugaban APC, Ganduje a jaridu

Nnamdi Kanu
Lauyoyi sun bukaci a saki Nnamdi Kanu. Hoto: Mazi Nnamdi Kanu Supporters
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lauyoyin Kanu sun tura takardar ne ga babban lauyan gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin neman sake Nnamdi Kanu

Shugaban lauyoyin Nnamdi Kanu, Barista Neameka Ejiafor ya ce sun tura takardar ne saboda kalaman da babban lauyan gwamnati ya yi.

Lauyan Kanu ya ce babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi ya ce bai da masaniya kan lamarin Kanu saboda haka suka rubuta masa takarda.

Lauyoyin sun ce suna fata idan ya karanta dalilan da suka nuna ya halasta a sake Nnamdi Kanu zai fahimta kuma ya ba da izinin sakinsa.

Takardar neman fito da Nnamdi Kanu

Ga abin da takardar ta kunsa:

"Mun rubuta takardar nan ne domin mu jawo hankalin ka kan abin da yake faruwa da Nnamdi Kanu."
"Mun tabbatar da cewa an boye gaskiyar lamarin ne daga gare ka saboda a hana ka tabbatar da adalci da kuma yin kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da izinin sake Nnamdi Kanu."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe za ta yi titin da kilomita 1 zai lakume sama da Naira biliyan 1

Kanu ya kasance a tsare tun da aka kamo shi daga kasar Kenya a shekarar 2021, amma a cikin wasikar sun bayyana dalilai guda tara da suka nuna ya kamata a sake shi, rahoton Channels Television.

An kaddamar da jirgin kasa a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufuri, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya tabbatar da cewa jirgin kasan Legas zuwa Kano zai fara aiki.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya ce an sanar da fara aikin jirgin kasan ne bayan an masa gyare-gyare na musamman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel