“Ya Fi Kowa Hazaƙa”: Gwamnan APC Ya Ba Ɗalibin Jami’a Kyautar Naira Miliyan 10
- Wani ɗalibin jami'ar Legas (LASU) mai suna Olaniyi Olawale ya samu kyautar Naira miliyan 10 daga Gwamna Babajide Sanwo-Olu
- Ɗalibin ya samu kyautar kuɗin saboda ya kammala karatunsa na ilimin akanta da makin CGPA 4.98, shi ne mafi hazaƙa a jami'ar
- Gwamnan na ya sanar da ba ɗalibin wannan kyautar a lokacin da ya halarci bikin yaye daliban jami'ar karo na 27 a yau Alhamis
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ba wani ɗalibi da ya kammala jami'ar Legas da sakamako mafi kyawu kyautar Naira miliyan 10.
Dalibin jami'ar LASU mafi hazaƙa a 2023
Sanwo-Olu ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a taron yaye daliban jami'ar Legas (LASU) karo na 27.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da babban mai tallafawa gwamnan kan soshiyal midiya, Jubril Gawat ya fitar a shafinsa na X, ɗalibin mai suna Olaniyi Olawale ya fita da CGPA na 4.98.
Jubril Gawat ya ce Olaniyi Olawale wanda ya kammala karatunsa a fannin ilimin akanta a zangon karatu na shekarar 2022/2023, ya samu kyautar ne saboda hazakarsa.
LASU: Gwamna ya ba mai hazaka N10m
Sanarwar mai taimakawa gwamnan ta ce:
"Gwamnan jihar Legas, Mr Babajide Sanwo-Olu ya ba Olaniyi Mubarak Olawale, daga sashen ilimin akanta kyautar N10m saboda zama mafi hazaƙa a jami'ar baya samun CGPA na 4.98.
"Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau a jami'ar jihar Legas (LASU) a taron yaye dalibanta karo na 27."
Duba bidiyon jawabin gwamnan a nan kasa:
An dakatar da daliba a makarantar Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa makarantar firamare da sakandare ta Ace da ke Abuja ta kori dalibar da mahaifinta ya lakadawa malama dukan tsiya.
An ruwaito cewa mahaifin dalibar ya jibgi malamar ne saboda zargin ta yiwa diyarsa gwale-gwale yayin da malamar ta yi ikirarin cewa dalibar ce ta zage ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng