'A Rage Ciki', An Bukaci 'Yan Majalisa Su Rage Albashinsu Domin a Samu Kudi

'A Rage Ciki', An Bukaci 'Yan Majalisa Su Rage Albashinsu Domin a Samu Kudi

  • An bawa 'yan majalisun jihohi da na tarayya shawara kan matakin rage albashinsu domin tallafawa tattalin arzikin Najeriya da ya fada cikin mummunan yanayi a yanzu
  • Shugaban kungiyar Patriotic Volunteers for Good Governance da ke rajin kare dabbaka shugabanci na gari, Alhaji Usman Alhaji ne ya bayar da shawarar yau a Kano
  • Ya ce yawan da albashin 'yan majalisun ya taimaka wajen matsalolin da ake fuskanta kan batun mafi karancin albashi a Najeriya, duk da ya caccaki kungiyar kwadago na neman N494,000

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Duba da yadda Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki, wata kungiya mai rajin inganta shugabanci na gari ta Patriotic Volunteers for Good Governance ta shawarci ‘yan majalisu kan hanyar da za su bi wurin taimakawa kasar.

Kara karanta wannan

Ruftawar mahakar ma'adani: An ceto wasu a galabaice, gwamnati ta dauki mataki

Shugaban kungiyar kuma tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ya ce hanya mai sauki da za su bi ita ce rage yawan albashi da alawus-alawus da suke karba daga asusun kasar nan.

Majalisa
Matsin tattalin arziki: An shawarci 'yan majalisa su rage albashinsu Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa kungiyar ta bayar da shawarar ga ‘yan majalisun tarayya da na jihohi ganin yadda kullum Najeriya ke bayyana halin da tattalin arziki ke ciki mara dadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin ‘yan majalisa ya kawo matsala

Tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ya bayyana cewa tsabar yawan albashin da ‘yan majalisu ke karba ne ya kawo cikas wajen amincewa da mafi karancin albashi.

Kungiyoyin kwadagon kasar nan sun nemi gwamnatin tarayya ta amince da N494,000 a matsayin mafi karancin albashi, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

“Kamata ya yi ‘yan siyasa su nuna dattako ta hanyar amincewa don kashin kansu su rage kudin da ake biyansu. Muna fatan a yi haka ne saboda matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki," inji Alhaji Usman Alhaji.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin janye harajin shigo da kaya, ana sa ran saukar farashin abinci

Tsohon sakataren gwamnatin ya kuma caccaki kungiyoyin kwadago kan bukatar da suka mika ga gwamnati, inda ya shawarce su da amincewa da N60,000 gudun ka da wadansu su rasa ayyukansu.

An samu sabani tsakanin 'yan majalisa

A baya mun kawo muku labarin cewa an samu sabani tsakanin 'yan majalisun Arewacin kasar nan da takwarorinsu na kudu kan dokar hana makiyaya kiwo a fadin kasar nan.

Sanatan jam'iyyar APC daga jihar Benue, Titus Tartenger Zam ne ya gabatar da kudurin da ya tsallake karatu na biyu, inda ya ce zai taimakawa makiyaya da sauran al'umar kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel