Magana Ta Ƙare: Minista Ya Mikawa Tinubu Lissafin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata

Magana Ta Ƙare: Minista Ya Mikawa Tinubu Lissafin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata

  • Ministan kudi, Wale Edun ya miƙawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan wa'adin sa'o'i 48 ya tattara bayanai ya miƙa masa
  • Ana tsammanin rahoton ya kunshi sabon albashi, yadda zai taɓa kasafin kuɗi da kuma adadin kundin da zai laƙume wajen aiwatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan kudi da harkokin tattalin arziƙi, Wale Edun ya miƙa lissafin sabon mafi karancin albashi ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Hakan ya biyo bayan wa'adin sa'o'i 48 da Bola Tinubu ya bai wa ministan domin ya gaggauta kawo masa kunshin duk wani abu da ya shafi sabon albashin.

Kara karanta wannan

"Karya ne," Gwamnati ta yi magana kan amincewa da biyan albashin akalla N105, 000

Wale Edun da Bola Tinubu.
Ministan kudi, Wale Edun ya mika kundin sabon mafi ƙarancin albashi ga Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Rahoton karin albashin ma'aikata

Mista Edun ya miƙa kunshin mafi karancin albashin kama daga adadin kuɗin da zai laƙume da kuma yadda za a aiwatar da shi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta tattaro cewa ana sa ran ƙunshin lissafin da ministan ya miƙa wa shugaban ƙasa ya haɗa da sabon mafi karancin albashi da yadda zai shafi kasafin kudi.

NLC ta buƙaci a warware abubuwa 2

Idan ba ku manta ba kungiyar kwadago ta fara yajin aikin a fadin kasar nan a ranakun Litinin da Talata kan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati.

Abu na biyu da ƴan kwadagon suka bukata daga gwamnatin tarayya shi ne soke ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi wa ƴan rukunin Band A a kwanakin baya.

Sai dai manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin na tsawon kwankai bayan sun tattauna da wakilan gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista ya mika mafi karancin albashin N105,000 ga Tinubu? an fayyace gaskiya

Sun janye yajin aikin ne domin sake komawa teburin tattaunawa da lalubo maslaha game da sabom albashin ma'aikata, The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya musanta ware kudin tallafin mai

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta musanta ware N5.4trn da nufin biyan tallafin man fetur a bana 2024 kamar yadda ake yaɗawa

Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bukaci jama'a su yi watsi da daftarin da ake yaɗawa wanda ya nuna cewa har yanzu ana biyan tallafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel