Kwale Kwale Ya Kife da Masu Tserewa Harin 'Yan Bindiga a Neja, Mutum 4 Sun Rasu
- Wasu mutane masu tserewa hare-haren ƴan bindiga sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalensu ya kife a tsakiyar Kogi a jihar Neja
- Mutum huɗu ne suka rasa rayukansu waɗanda suka fito daga ƙauyen Gurmana a ƙaramar hukumar Shiroro sakamakon aukuwar lamarin
- Kwale-kwalen ya kife ne dai yayin da mutanen suke dawowa zuwa ƙauyen nasu bayan sun je ɓuya a wani tsibiri da ke tsakiyar kogin Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wani kwale-kwale da ke ɗauke da wasu mazauna ƙauyukan da ke tserewa hare-haren ƴan bindiga a jihar Neja ya kife.
Mutanen dai sun fito ne daga ƙauyen Gurmana da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Mutum nawa suka rasu a Neja?
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa bayan kifewar kwale-kwalen, mutum huɗu sun rasa rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen ƙauyen sun gudu zuwa wani tsibiri ne domin buya daga ƴan bindiga a daren ranar Laraba bayan ƴan bindigan sun kawo hari.
Kifewar kwale-kwalen ta auku ne a ranar Alhamis lokacin da suke dawowa bayan da ƴan bindigan suka gama kai farmaki a ƙauyukan.
Mutane sun gudu kan harin ƴan bindiga
An tattaro cewa mutanen ƙauyen suna zuwa tsibirin ne da ke tsakiyar kogin Kaduna domin ɓuya daga ƴan bindigan da suke jin tsoron kogin.
Ƴan bindigan sun kashe mutum uku a hare-haren na daren jiya, sannan sun sace shanu masu yawa tare da yin awon gaba da mutane da dama a Bassa kusa da Gurmana.
Jihar Neja dai na ɗaya daga cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya waɗanda ke fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga waɗanda suka jawo asarar rayukan mutane masu yawa.
Ƴan bindiga sun sace mutane a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 30 a ƙauyen Kakuru da ke ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.
Har ila yau a wani harin na daban, ƴan bindiga sun sace mutane 26 daga ƙauyen Adogo Mallam, shi kuma a ƙaramar hukumar Tunga duk a Neja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng