Ana Fama da Rigimar Sarauta, Sarki Sanusi II Ya Gana da Wasu Manyan Mutane a Kano
- Ƙungiyar likitocin fata ta Najeriya ta ziyarci Sarki Muhammasu Sanusi II a fadarsa da ke birnin Kano ranar Laraba
- Shugaban ƙungiyar, Farfesa Shehu Yusuf ne ya jagoranci tawagar likitocin zuwa fadar sarkin Kano da ke Kofar Kudu
- Wannan ziyara na zuwa ne yayin da hakimai da sauran manyan mutane ke zuwa kai gaisuwa da mubayi'a ga sarkin bayan mayar da shi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya karɓi bakunci ƙungiyar likitocin fata ta Najeriya a fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Ƙungiyar likitocin karƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Shehu Yusuf, ta kai ziyara ga sarkin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, 2024.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalipha Muhammadu Sanusi II ya karɓi bakuncin ƙungiyar likitocin fata ta Najeriya karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Farfesa Shehu Yusuf," in ji sanarwar.
Muhammadu Sanusi II na samun karɓuwa
Wannan ziyara ta biyo bayan ziyarar da ƴaƴan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi suka kai wa basaraken ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.
Haka nan kuma Sarkin Gwandu, Muhammad Ilyasu Bahar ya aike da saƙon taya murna ga Sanusi II bisa mayar da shi kan karagar sarauta.
Har yanzun dai ana ci gaba da taƙaddama kan kujerar sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Shari'ar sarauta: An jibge jami'an tsaro a kotu
Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa a yau Alhamis, babbar kotun tarayya mai zama a Kano za ta sake zama kan shari'ar masarautar Kano.
Tuni dai hukumomin tsaro suka jibge dakaru domin tabbatar da doka da oda a harabar kotun da kuma kammala zaman shari'ar lafiya.
An tattaro cewa jami'an ƴan sanda da DSS sun turke motocinsu a wurare masu muhimmanci da ke kusa da kotun kuma sun hana zirga-zirga.
Gwamnatin Kano ta tashi ƴan kasuwa
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano ta umarci ƴan kasuwa su tashi daga wuraren da aka kebe domin shakatawa da hutawa a faɗin jihar.
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Nasiru Sule Garo, ya ce mutane sun mayar da wasu lambunan shaƙatawa wurin kasuwanci ba tare da izini ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng