Komai Nisan Jifa: Matashi ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro Bayan Shekaru da Damfara

Komai Nisan Jifa: Matashi ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro Bayan Shekaru da Damfara

  • Wani matashi da ya yi damfarar motar N30m daga Amurka tun a shekarar 2016 ya fada komar rundunar 'yan sandan jihar Legas da ke shiyya ta biyu da ke Onikan
  • Wannan ya biyo bayan korafin da wanda aka damfara mai lasisin sayar da motoci a can kasar, Adesuwa Ogizie ta shigar gaban rundunar yan sandan
  • Jami’ar hulda da jama’a ta shiyyar, SP Umma Ayuba ta ce an kama Olawuyi kuma ya amsa laifinsa, tare da bayyana musu cewa a wancan lokaci yana damfara ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos- Wani matashi da ya kware wajen damfarar jama’a ta kafar intanet Joshua Olawuyi, ya fada hannun jami’an tsaron shiyya ta biyu dake Onikan a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta yi namijin aiki, an damke miyagu iri iri

An cafke matashin ne bayan ya yi kwanta-kwanta tare da damfarar mota da ta kai zunzurutun kudi na N30m jim kadan bayan karbar koken wacce aka damfara.

Lagos
An kama matashin da ya yi damfarar motar N30m Hoto: Lagos State Police Command
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa jami’ar hulda da jama’a ta shiyyar, SP Umma Ayuba ta tabbatar da cafke matashin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damfara: Yadda aka kama Joshua Olawuyi

Jaridar Punch News ta tattaro cewa SP Umma Ayuba ta bayyana cewa shiyyar rundunar karkashin Olatoye Durosinmi sun jagoranci cafke Joshua Olawuyi bayan Adesuwa Ogizie, ta mika musu kokenta.

Adesuwa Ogizie, mazauniyar kasar Amurka ce da ke da lasisin cinikin motoci, wanda ta haka ne matashin ya damfare ta mota kirar Mercedes Benz GLE 350 da kudinta ya kai N30m a shekarar 2016.

Dan damfara ya shiga hannu

Matashin ya sayi motar, sannan ya shaidawa Ogizie cewa wani dan uwansa ne zai ba ta kudin. A karshe sai bayan an biya ta ne ta ga ba daidai ba.

Kara karanta wannan

NSCDC a Kano ta damke masu addabar al'ummar jihar da sace-sace

Bayan kama matashin ne ya shaidawa jami'an 'yan sanda cewa lokacin da ya sayi motar yana damfara ta kafar intanet, inda ya ce tuni ya sayar da motar.

An sace jaririn wata daya a Legas

A baya mun kawo muku rahoton yadda wata matashiya ta sace jaririn wata daya lokacin da mahaifiyarsa ke bacci, kuma ta ajiye yaron a gefenta.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya ce sun kama matar mai suna Blessing wacce tuni ta fara shaidawa mutane danta ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel