Makarantar Abuja Ta Ɗauki Mataki Kan Ɗalibar da Mahaifinta Ya Lakaɗawa Malama Duka

Makarantar Abuja Ta Ɗauki Mataki Kan Ɗalibar da Mahaifinta Ya Lakaɗawa Malama Duka

  • Makarantar firamare da sakandare ta Ace da ke Garki a Abuja ta dauki mataki kan ɗalibar da mahaifinta ya lakaɗawa malama duka
  • A makon da ya gabata muka ruwaito cewa wani Muhammad Jimeta ya shiga makarantar ya jibji Malama Sekinat Adedeji
  • Shugaban makarantar, Alhaji Aminu Kani ya ce sun dakatar da ɗalibar, Karima Muhammad Jimeta da Malama Sekinat Adedeji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Makarantar Abuja da wani mahaifi ya shiga ya lakaɗawa wata malama duka saboda ta ladabtar da yarinyarsa ta dauki mataki.

A makon da ya gabata ne wani mahaifi ya shiga makarantar Aces da ke Area 2, Garki, Abuja ya lakaɗawa malama duka saboda ta horar da ɗiyarsa.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Makarantar Abuja ta yi magana kan dukan malamarta.
Makarantar Abuja ta dakatar da dalibar da mahaifinta ya doki malama. Hoto: James Marshall
Asali: Getty Images

A matakin da shugaba makarantar, Alhaji Aminu Kani ya dauka, ya ce makarantar ta kori ɗalibar da malamar da abin ya shafa, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifi ya lakadawa malamar makaranta duka

A ranar 29 ga watan Mayu muka ruwaito wani mahaifin dalibin makarantar, Muhammad Jimeta ya shiga har cikin makarantar ya doki Malama Sekinat Adedeji.

Sekinat Adedeji ta ce tana cikin shayar da jaririnta ɗan wata uku Jimeta ya rufe ta da duka saboda ta ladabtar da ɗiyarsa, Karima Muhammad Jimeta, 'yar aji uku a firamare.

An dai zargi ita Karima da ƙin mayar da hankali a karatu, da kuma yawan zagin mutane, tare da cewa mahaifin ya dauki hukunci a hannu.

Mahaifin da ya yi duka a makaranta

Sai dai da ya ke martani kan ikirarin Malama Sekinat, Muhammad Jimeta ya zargi malamar da hantarar 'yarsa, kuma ba tun yanzu ta fara ba, inji rahoto The Punch.

Kara karanta wannan

Bayan tsawon kwanaki 75, Sanata Abdul Ningi ya koma zaman majalisa

Jimeta wanda ya ce ya shafe shekaru 20 yana koyarwa ya zargi malamar da yiwa 'yarsa gwale-gwale a kan laifin da bai taka kara ya karya ba.

Makarantar Abuja ta dauki mataki

Da ya ke martani kan abin da ya faru, shugaban makarantar, Alhaji Kani ya ce ba ya gari lokacin da abin ya faru amma za su yi bincike.

Daga baya ya ce sun yanke shawarar korar ɗaliba da malamar da abin ya shafa har zuwa lokacin da za su kammala bincike.

"Ga mahaifin, bai kamata ya zo har cikin makaranta ya doki malamar ba, me ya ke son koyar da 'yayansa kenan? Ita kuma malamar me ya kai ta har ta doki 'yayan mutane?".

- Alhaji Kani

Ana zargin El-Rufai ya karkatar da kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai da karkatar da akalla N423bn.

Kara karanta wannan

InnaliLahi: Mutane 30 sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa a Arewa

Kwamitin da majalisar ta kafa domin ya binciki gwamnatin El-Rufai ya nemi da a tuhumi tsohon gwamnan da mukarrabansa kuma a gurfanar da su gaban kotu kan almundahana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel