El Rufai: Dan Majalisa Ya Bayyana Yadda Tsohon Gwamna Ya Bar Kaduna Cikin Matsala

El Rufai: Dan Majalisa Ya Bayyana Yadda Tsohon Gwamna Ya Bar Kaduna Cikin Matsala

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zama abin magana bayan majalisar dokokin jihar ta yi bincike a kan gwamnatinsa
  • Shugaban kwamitin binciken ya yi zargin cewa tsohon gwamnan ya bar kaso 60% na ayyukan da ba a kammala ba duk da an gama biyan kuɗi
  • Ya yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta karɓo basussuka ba tare da yin wani abu da su ba sannan cike ta ke da cin hanci da rashawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wani ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna, Henry Marah, ya yi zargin cewa gwamnatin Nasir Ahmad El-Rufai ta bar kusan kaso 60% na ayyukan da ba a kammala ba.

Ɗan majalisan shi ne shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar Kaduna dake binciken gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan

"Kanku ake ji": El-Rufai ya bugi kirji, ya yi zazzafan martani kan zargin badaƙala a Kaduna

Dan majalisa ya zargi El-Rufai da cin hanci
Dan majalisa ya zargi El-Rufai da karbo bashi ba tare da yin aiki ba Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Wane zargi aka yi kan gwamnatin El-Rufai?

Ya bayyana cewa kaso 60% na ayyukan da gwamnatin ta bari, an kammala biyan kuɗadensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Henry Marah ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ake hira da shi a tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba.

"A lokacin da El-Rufai ya hau mulki a 2015, dukkanin bashin cikin gida da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo, ta biya shi. Ya zo ya tarar babu bashin ko sisin kwabo sannan an bar masa N3bn domin ya fara gwamnatinsa."
"Yanzu je ka duba ka gani a bayanan miƙa mulki na El-Rufai bashin nawa ya bari. Sannan kuɗaɗen da ya karɓa domin yin ayyukan, sama da kaso 60% na waɗannan ayyukan an yi watsi da su."
"Sai ya ɗauki jihar Kaduna kusan shekara 20 kafin ta kammala abin da ya bari. Saboda haka ina gaskiyar take a nan?"

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan CBN ya shiga tasku, kotu ta ƙwace manyan kadarorinsa na N11.1bn

- Henry Marah

Nasir El-Rufai ya ci bashi babu aiki

Ya yi zargin cewa an karɓo basussuka masu yawa domin gudanar da ayyuka amma ba a yi ayyukan ba kuma kuɗaɗen sun yi ɓatan dabo.

A cewar ɗan majalisar an karɓo kuɗaɗe ba tare da yin wani abu da su ba. Ya yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai cike ta ke da cin hanci sannan ta wawushe asusun jihar.

Ɗan majalisar ya yi iƙirarin cewa wasu basussukan da gwamnatin El-Rufai ta karɓo ba majalisar ta amince da su ba, kuma an yi sa hannun jabu na wasu ƴan majalisar domin amincewa da basussukan.

Yaushe za a gayyaci El-Rufai

Ya ce duk waɗanda suka yi aiki a gwamnatin da ta shuɗe, sa hannunsu ya bayyana a takardun da suka dace, an gayyace su kuma sun bayyana a gaban kwamitin amma ba a gayyaci El-Rufai ba.

Sai dai, Henry Marah ya ce za a ba El-Rufai damar kare kansa. Ya ƙara da cewa an aike da rahoton kwamitin ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɗaukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tafka 'aika aika': Ana zargin tsohon gwamna ya karkatar da N423bn

Malam El-Rufai ya magantu kan bincikensa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi martani kan zargin karkatar da ake yiwa gwamnatinsa.

Tsohon ministan na babban birnin tarayya Abuja ya yi fatali da rahoton majalisar dokokin kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel